Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Zariya

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Zariya

  • Matsalolin tsaro na ƙara tabarbarewa a Arewacin Najeriya musamman yankin arewa maso yamma
  • Kwana ɗaya bayan tare hanyar Zaria-Kaduna, wasu yan bindiga sun shiga ƙauyukan Zariya, sun sace mutane akalla biyar
  • Duk da har yanzun hukumar yan sandan jihar ba ta ce komai ba, amma mazauna yankunan sun tabbatar da faruwar lamarin

Zaria, Kaduna - Wasu yan bindiga sun sake sace mutum 5 a ƙauyukan Dallatu da Kasuwar Da'a dake Dutsen Abba a ƙaramar hukumar Zariya, jihar Kaduna.

Dailytrust tace wannan na zuwa ne awanni 24 kacal bayan wasu yan bindiga sun tare babbar hanyar Zariya-Kaduna, kuma suka kashe mutum 3, suka sace wasu da dama.

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Zariya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Har yanzun rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna ba ta ce uffan ba kan sabon harin da yan bindiga suka kai ƙauyuka biyu a Zariya.

Kara karanta wannan

Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn

Yadda lamarin ya faru da tsakar dare

Amma wasu mazauna yankin, sun bayyana cewa yan bindigan sun farmaki kauyen Dallatu da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka sace mutum biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga nan yan bindigan suka zarce zuwa ƙauyen Kasuwar Da'a, inda suka tasa keyar wasu mutum shida, daga cikinsu har da kananan yara uku.

Sai dai wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa yan bindigan sun sako kananan yaran guda uku ranar Laraba da safe, suka rike sauran mutum 5.

Harin Zariya-Kaduna

A baya-bayan nan yan bindiga sun farmaki matafiya a kan hanyar Zariya zuwa Kaduna inda suka kashe akalla mutum uku.

Legit.ng Hausa ta gano cewa daga cikin waɗan da maharan suka kashe har da ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna.

A cewar wasu daga cikin mutanen da suka tsira, dakarun soji sun kawo ɗauki har suka ceto wasu mutane, amma maharan sun tasa matafiya da dama.

Kara karanta wannan

A shekara 90, Sarkin Daura ya auri tsaleliyar Amarya 'yar shekara 20

A wani labarin na daban kuma Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Masari ya bayyana mutanen da suka kashe kwamishina a Katsina

Bayan kashe kwamishinan kimiyya da fasaha, Dakta Rabe Nasir, ranar Laraba, gwamnan Katsina , Aminu Masari, yace kisan ba shi da alaƙa da yan bindiga.

Punch ta rahoto gwamnan na cewa ya zama wajibi baki ɗaya jihohin arewa ta yamma su haɗa karfi da ƙarfe wajen magance ƙalubalen tsaro da ya addabi yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel