Da Dumi-Dumi: Miyagun Yan bindiga sun sake awon gaba da wani Sarki a Najeriya

Da Dumi-Dumi: Miyagun Yan bindiga sun sake awon gaba da wani Sarki a Najeriya

  • Wasu yan bindiga da ba'a gano su ba, sun sace basaraken gargajiya a yankin karamar hukumar Ehime Mbano, jihar Imo
  • Wannan na zuwa kwanaki kaɗan bayan wasu mahara sun sace sarakuna biyu a karamar hukumar Okigwe, sun kona fadarsu
  • Hukumar yan sandan jihar ba ta ce komai ba game da lamarin, amma wata majiya ta tabbatar da faruwarsa

Imo - Tabarbarewar tsaro da kuma garkuwa da sarakunan gargajiya ya cigaba a jihar Imo ranar Laraba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wasu tsagerun yan bindiga da ba'a gano ko su waye ba sun yi awon gaba da basaraken yankin Umuezeala-Ama, dake karamar hukumar Ehime Mbano, jihar Imo.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun samu nasarar iza keyar sarkin ne a kasuwar Nkwo-Umuezeala.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

Jihar Imo
Da Dumi-Dumi: Miyagun Yan bindiga sun sake awon gaba da wani Sarki a Najeriya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata majiya mai karfi ta shaida wa manema labarai cewa basaraken ya fita zuwa yankin ne domin ɗakko matarsa da ta halarci wani taro.

Vanguard ta rahoto majiyar tace:

"Sun shigo kasuwar inda suka umarci basaraken ya shiga motarsu. Ba shi da wani zaɓe da ya wuce ya musu biyayya."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, Michael Abattam, yace yana cikin taro ne dan haka ba zai iya tabbatar da lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi.

Sai dai wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu yan ta'adda sun sace sarakunan gargajiya biyu a jihar Imo.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa bayan sace sarakunan, maharan sun kone fadarsu da kuma motocin su.

Shin an kubutar da su?

Kara karanta wannan

Sabon Hari: Tsagerun yan bindiga sun sake awon gaba da mutane a Zariya jihar Kaduna

Har yanzun da muke tattara wannan rahoton, ɗaya daga cikin sarakunan, Eze Paul Ogbu na masarautar Ihitte Ihube a karamar hukumar Okigwe na hannun yan bindigan.

Amma shi wanda aka sace su kusan lokaci ɗaya, Eze Acho Ndukwe na masarautar Amagu Ihube a karamar hukumar Okigwe, ya kubuta ranar Litinin.

A wani labarin na daban kuma Miyagun yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Zariya

Wasu yan bindiga sun sake sace mutum 5 a ƙauyukan Dallatu da Kasuwar Da'a dake Dutsen Abba a ƙaramar hukumar Zariya, jihar Kaduna.

Dailytrust tace wannan na zuwa ne awanni 24 kacal bayan wasu yan bindiga sun tare babbar hanyar Zariya-Kaduna, kuma suka kashe mutum 3, suka sace wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel