'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar aure tare da wasu mutum 4 a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa

'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar aure tare da wasu mutum 4 a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa

  • ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata matar aure mai shekaru 38, Hulaira Audu da wasu mutane hudu a anguwar Okatubo da ke karamar hukumar Kogi a cikin jihar Kogi
  • Wani dan’uwanta, Salihu ne ya bayyana yadda lamarin ya auku a ranar Lahadi da misalin karfe 6pm inda ya ce su na hanyar dawowa daga kasuwar Kotonkarfe
  • A cewarsa su na hanyar dawowa daga kasuwar, ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji da bindigogi su ka bayyana daga daji su ka dakatar da su

Kogi - ‘Yan bindiga sun sace wata matar aure mai shekaru 38, Hulaira Audu da wasu mutane hudu a anguwar Okatubo da ke karamar hukumar Kogi cikin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

Dan’uwan wacce lamarin ya ritsa da ita, Salihu ne ya yi bayani akan yadda mummunan al’amarin ya auku a ranar Lahadi da misalin karfe 6pm yayin da su ke hanyar dawowa daga kasuwar Kotonkarfe da ke anguwar.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar aure tare da wasu mutane 4 a hanysarsu ta dawowa daga kasuwa
Masu garkuwa sun sace matar aure da mutum 4 a Kogi. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana yadda su ke cikin mota a hanyar dawowa gida yayin da ‘yan bindigan su ka bayyana rike da bindigogi kirar AK-47 daga daji su ka dakatar da su.

Ya ce sun bayyana ne sanye da kayan sojoji

Kamar yadda ya shaida:

“Su na gab da isa kauyen kusa da mu, Adingere, lokacin da masu garkuwa da mutanen sanye da kayan sojoji su ka dakatar da su. Sun wuce da matar da wasu ‘yan kasuwa hudu tare da direban motar.”

Daily Trust ta gano yadda har yanzu ‘yan bindigan ba su kira kowa ba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Wani Dan Sa Kai wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da satar matar auren da sauran mutane hudun.

A cewarsa, yanzu haka ‘Yan Sa Kai sun sanar da takwarorinsu da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa don a fara bincika dajin don ceto wadanda aka sace.

Kauyen kusa da jihar Nasarawa ya ke

“Kauyen ya na da iyaka da jihar Nasarawa,” a cewarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, CSP Williams Ovye Aya bai amsa kiran wayar da wakilin Daily Trust ya masa ba, sannan bai bayar da amsar sakon da aka tura masa ba dangane da satar mutanen.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga daga Zamfara sun kutsa Filato, sun kai farmaki, sun hallaka mutane 10

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel