Yan bindiga sun sake kai sabon hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja, sun kashe mutane

Yan bindiga sun sake kai sabon hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja, sun kashe mutane

  • Duk da jami'an tsaron da aka jibge a kan hanyar Kaduna-Abuja, yan bindiga na cigaba da aikata ta'addanci a titin
  • A ranar Lahadi da ta gabata, wasu yan bindiga sun farmaki matafiya a titin Kaduna-Abuja, sun kashe mutum biyu
  • Wani da abun ya faru a idon sa, ya bayyana cewa ga dukkan alamu maharan ba satar mutane suka zo ba, duba da yadda suke harbi kan mai uwa da wabi

Kaduna - Wasu miyagun yan bindiga sun bude wuta kan matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi da daddare.

Rahotanni sun tabbatar da cewa harin wanda ya auku da misalin karfe 10:30 na dare zuwa 11:00, maharan sun bindige mutum biyu har lahira.

Ɗaya daga wanda abun ya rutsa da su, Ibrahim Umar Bari, wanda ya zayyana abinda ya faru a shafin Facebook, yace maharan da niyyar kisa kawai suka zo.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun kai hari babbar hedkwatar yan sanda ta jiha

Yan bindiga
Yan bindiga sun sake kai sabon hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja, sun kashe mutane Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yayin harin na tsawon minti 30 maharan ba su samu wata tirjiya daga jami'an tsaro ba, duk da kasancewar wurin na kusa da madakatar bincike, inji shi.

Yadda lamarin ya faru

Malam Umar ya bayyana cewa tun yan bindigan na da nisan mita 300 suka hange su, saboda haka kafin su kariso wurin motar su, duk suka tsere.

Yace:

"Tun da nake ban taɓa ganin harsashi na yawo a sama ba sai jiya, ga dukkan alamu ba mutane suka zo ɗiba ba, kashe wa kawai ya kawo su."
"Tsakanin mu da su bai fi mita 300, shiyasa kafin su iso motar mu, muka tsere. Har kusa da maɓoyarmu suka zo suna harbi, da alamu bindigun su ba irin na mutanen (Jami'an tsaro) bane."
"Bani da tabbacin ko sun sace mutane, amma tabbas sun fasa tayoyin motoci da harbi kuma sun kashe mutum biyu a wata mota kirar J5, kamar yadda muka samu labari bayan wuce motar a kan hanya."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga daga Zamfara sun kutsa Filato, sun kai farmaki, sun hallaka mutane 10

Zamu kawo karshen matsalar tsaro - FG

A wani labarin na daban kuma Fadar shugaban kasa ta bayyana abubuwan da Buhari ke yi na kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa.

Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel