Zaratan 'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda 2 a Jihar Kaduna

Zaratan 'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda 2 a Jihar Kaduna

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana yadda ta halaka wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne guda biyu a kauyen Riheyi da ke karamar hukumar Giwa
  • Jami’in hulda da jama’an rundunar na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya bayyana hakan ta wata takarda da rundunar ta saki a ranar Talata a Kaduna
  • A cewar Jalige, a ranar Litinin da misalin karfe 4:30pm lamarin ya faru, inda ya ce sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan

Jihar Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarar halaka ‘yan bindiga a kauyen Riheyi da ke wuraren Fatika a karamar hukumar Giwa, The Nation ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, ASP Mohammed Jalige ya bayyana hakan ta wata takarda ta ranar Talata a Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga daga Zamfara sun kutsa Filato, sun kai farmaki, sun hallaka mutane 10

'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda a Jihar Kaduna
Yan sanda sun kashe yan ta'adda biyu a Kaduna. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

A cewar Jalige, a ranar Litinin da misalin karfe 4:30pm, jami’an rundunar da ke 47 PMF Squadron, Zaria, sun ci karo da ‘yan bindiga a kauyen.

The Nation ta ruwaito yadda lamarin ya auku ne yayin da jami’an su ke tsaka da sintiri a cikin karamar hukumar Giwa.

Sai da su ka yi musayar wuta

Jalige ya ce lamarin ya janyo musayar wuta tsakanin ‘yan sandan da ‘yan bindigan.

Kamar yadda ya shaida:

“Sakamakon jajircewar rundunar ‘yan sandan, ta samu nasarar halaka ‘yan bindiga biyu sannan sun kwace bindigogi kirar AK47 guda biyu tare da wani babur a hannun ‘yan bindiga.”

Jalige ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Mudassiru Abdullahi ya yaba wa jarumtar ‘yan sandan da su ka nuna jajircewa da kwarewarsu a kan ayyukansu.

Kara karanta wannan

Bayan Ƙona Fasinjoji Da Ransu, Ƴan Bindiga Sun Sake Zubar Da Jini a Wani Gari a Sokoto

Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci ‘yan sanda da su dinga sintiri

Ya kuma bukaci sauran jami’an rundunar da su kwafi irin wannan salo na sintiri a bangarorin da su ke aiki.

Kakakin ya ce Kwamishinan ya bukaci su jajirce sakamakon yadda bukukuwan addinai su ke kusa, don ganin sun dakatar da duk wani ta’addanci.

Kamar yadda Jalige ya shaida:

“Kwamishinan ‘yan sanda ya ce, kowa ya san ‘yan sanda ne su ke da alhakin yaki da ta’addancin cikin kasa, akwai bukatar jami’an su jajirce.
“Ya ja kunne, inda ya ce idonsa na sanye akan duk wani jami’in rundunar da ba ya tsayawa akan aikinsa, kuma zai dauki mummunan mataki akansa.”

Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai

A wani labarin mai alaka da wannan, Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojoin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Sojoji sun cafke Shugaban ‘Yan banga bisa zargin alaka da ‘Yan bindiga

Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel