Bayan Ƙona Fasinjoji Da Ransu, Ƴan Bindiga Sun Sake Zubar Da Jini a Wani Gari a Sokoto

Bayan Ƙona Fasinjoji Da Ransu, Ƴan Bindiga Sun Sake Zubar Da Jini a Wani Gari a Sokoto

  • Wasu ‘yan bindiga sun kara kai farmaki kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto inda su ka halaka mutane 3
  • Lamarin ya auku ne bayan sa’o’i uku da gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ya bar yankin, bayan raba wa ‘yan uwan ko wanne mamaci N250,000
  • An samu rahoto akan yadda ‘yan bindigan su ka afka kauyen da misalin karfe 8 na dare na yammacin Alhamis su na ta harbi ko ta ina

Sokoto - Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun afka kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar inda su ka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.

Harin ya auku ne bayan sa’o’i kadan da gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ya kai ziyara yankin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

Bayan Ƙona Fasinjoji Da Ransu, Ƴan Bindiga Sun Sake Zubar Da Jini a Wani Gari a Sokoto
'Yan Bindiga Sun Sake Zubar Da Jini a Wani Gari a Sokoto. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Tambuwal ya je ta’aziyya gami da jaje ne ga ‘yan uwan wadanda mummunan lamarin ya ritsa da su inda ‘yan bindiga a daidai titin Sabon Birni-Isa su ka babbaka su kurmus ranar Litinin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya raba wa ‘yan uwan ko wanne mamaci N250,000.

Da misalin 8 na dare suka kai farmakin

Wakilin Daily Trust ya tattaro bayanai akan yadda su ka afka kauyen da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis, suna ta harbi ko ta ina.

A cewar wani mazaunin yankin:

“Sun zo jiya da dare mu na tsaka da sallah inda su ka dinga harbe-harbe. Sun halaka mutane uku sannan sun raunana wasu wadanda yanzu su na asibiti.”

Ba a samu damar tattaunawa da kakakin rundunar ‘yan sanda ba

Ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Sanusi Abubakar ba.

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Mutane da dama da ke fadin kasar nan sun dinga cece-kuce akan halaka matafiyan.

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

A baya, Kwamishinan 'yan sandan Jihar Sokoto, CP Kamaludeen Okunola, ya tabbatar da cewa an kashe mutum 23 yayin harin da aka kai wa matafiya a Angwan Bawa a karamar hukumar Sabon Birni na Jihar.

Okunola, wanda ya tabbatar da adadin a jiya, bayan taron tsaro da Gwamna Aminu Tambuwal, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, ya kara da cewa an tura jami'ai su binciko wadanda suka aikata.

Kakakin yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar, ya bada labarin yadda yan bindigan suka kai wa motar da ke dauke da fasinjoji 42 hari, hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 18.

Asali: Legit.ng

Online view pixel