Labari Da Duminsa: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba Da Hakimi a Arewa

Labari Da Duminsa: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba Da Hakimi a Arewa

  • Wasu bata gari da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace hakimin Mogaji Erubu a Masarautar Ilorin
  • An sace Dokta Zubair Folorunsho Erubu ne a hanyarsa ta zuwa gonarsa tsakanin Ilorin da Afon a karamar hukumar Asa
  • Rundunar yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin mai magana da yawun yan sanda, Okasanmi Ajayi

Kwara, Ilorin - Masu garkuwa da mutane sun sace Mogaji Erubu a Masarautar Ilorin ta jihar Kwara, Dokta Zubair Folorunsho Erubu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An rahoto cewa an sace Erubu ne a hanyarsa ta zuwa gonarsa tsakanin Ilorin da Afon a karamar hukumar Asa a jihar a ranar Alhamis.

Labari Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Hakimi a Kwara
Masu Garkuwa Sun Sace Hakimi a Kwara. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kwana Ɗaya Bayan Sace Basarake, An Tsinci Gawarsa a Tsakiyar Kasuwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Erubu, dan shekaru 60, tsohon sakataren dindindin ne a gwamnatin jihar sannan tsohon babban jami'i a asibitin gwamnatin jihar Kwara.

'Yan sanda sun tabbatar da sace basaraken

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin mai magana da yawun yan sanda, Okasanmi Ajayi.

Kwamishinan yan sandan, Tuesday Assayomo, ya bada umurnin a fara bincike nan take, tare da ceto wanda aka sace a kuma kamo masu garkuwar su girbi abin da suka shuka.

Yan Najeriya na cigaba da nuna damuwarsu kan yawaitar hare-hare a kasar inda suke kira ga gwamnati ta dauki matakin dakile harin.

Kwana Ɗaya Bayan Sace Basarake, An Tsinci Gawarsa a Tsakiyar Kasuwa

A wani labarin, mutanen tsohuwar masarautar Atta da ke karamar hukumar Njaba ta jihar Imo sun tsunduma zaman makoki bayan kisar gillar da aka yi wa sarkinsu, Eze Edwin Azike.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya yi tsokaci kan kisan matafiya a jihar Sokoto

The Punch ta rahoto cewa an tsinci gawar Azike a filin kasuwar garin a safiyar ranar Juma'a, 10 ga watan Disamba.

An tattaro bayanai cewa an kashe basaraken ne bayan an sace shi daga fadarsa a ranar Alhamis 9 ga watan Disamba.

Wata majiya wacce ta nemi a boye sunanta ta shaidawa jaridar cewa an bindige mutane hudu har lahira a ranar Alhamis bayan an sace basaraken.

Asali: Legit.ng

Online view pixel