Yanzu-Yanzu: Kwana Ɗaya Bayan Sace Basarake, An Tsinci Gawarsa a Tsakiyar Kasuwa

Yanzu-Yanzu: Kwana Ɗaya Bayan Sace Basarake, An Tsinci Gawarsa a Tsakiyar Kasuwa

  • Mutanen wani gari a kudu maso gabashin Najeriya na cikin firgici da alhini bayan an gano gawar sarkinsu a ranar Juma'a 10 ga watan Disamba
  • Yan bindiga ne suka yi wa basaraken na tsohuwar masarautar Atta da ke karamar hukumar Njaba kisar gilla
  • An sace marigayin basaraken ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba bayan wasu mahara sun kutsa fadarsa sun dauke shi

Njaba, Imo - Mutanen tsohuwar masarautar Atta da ke karamar hukumar Njaba ta jihar Imo sun tsunduma zaman makoki bayan kisar gillar da aka yi wa sarkinsu, Eze Edwin Azike.

The Punch ta rahoto cewa an tsinci gawar Azike a filin kasuwar garin a safiyar ranar Juma'a, 10 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun kutsa har cikin fada, sun yi awon gaba da Sarki mai daraja

Yanzu-Yanzu: An Tsinci Gawar Basaraken Da Aka Sace a Tsakiyar Kasuwa
Yan bindiga sun kashe basarake a karamar hukumar Njaba, jihar Imo. Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

An tattaro bayanai cewa an kashe basaraken ne bayan an sace shi daga fadarsa a ranar Alhamis 9 ga watan Disamba.

Wata majiya wacce ta nemi a boye sunanta ta shaidawa jaridar cewa an bindige mutane hudu har lahira a ranar Alhamis bayan an sace basaraken.

Akasin abin da The Punch ta ruwaito, The Nation ta bayyana cewa an bindige basaraken ne a kai sannan aka ajiye gawarsa a cikin mota.

Micheal Abattam, mai magana da yawun yan sandan jihar yayin tabbatar da afkuwar lamarin ya ce an tsinci gawar basaraken a cikin mota.

Majalisar Sarakuna ta yi Alla-wadai ta kisar Azike

Eze Emma Okeke, shugaban majalisar sarakuna da yan sandan unguwa ya ce sarakunan kudu maso gabas suna bakin cikin mutuwar abokin aikinsu.

Kara karanta wannan

Maza sun kwanta: An gudanar da Jana'izar tsohon Hafsan Sojoji a Sultan Bello Kaduna

Yayin da ya ke bayyana kisar sarkin a matsayin abin Alla-wadai, Okeke yana mamakin abin da yasa ake farautar masu sarautan gargajiya a yankin.

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

A wani labarin, Kwamishinan 'yan sandan Jihar Sokoto, CP Kamaludeen Okunola, ya tabbatar da cewa an kashe mutum 23 yayin harin da aka kai wa matafiya a Angwan Bawa a karamar hukumar Sabon Birni na Jihar.

Okunola, wanda ya tabbatar da adadin a jiya, bayan taron tsaro da Gwamna Aminu Tambuwal, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, ya kara da cewa an tura jami'ai su binciko wadanda suka aikata.

Kakakin yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar, ya bada labarin yadda yan bindigan suka kai wa motar da ke dauke da fasinjoji 42 hari, hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 18.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fattataki 'yan bindiga, sun ceto wani matashi dan shekara 17 a Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel