Sarkin Musulmi ya yi tsokaci kan kisan matafiya a jihar Sokoto

Sarkin Musulmi ya yi tsokaci kan kisan matafiya a jihar Sokoto

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi nasa tsokacin kan kashe-kashen dake gudana musamman a Arewacin Najeriya
  • A jawabin da yayi ranar Alhamis, Sarkin ya bayyana cewa babu ranar Allah da ba'a kashe mutane a Arewa
  • Sultan ya yi kira da mazauna jihohin Arewa su daina tsoron mutuwa sakamakon hare-haren yan bindiga

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III a ranar Alhamis, 9 ga Disamba, ya yi Alla-wadai da kisan gillan da ake yiwa yan Najeriya, musamman a yankin Arewa.

Sarkin yace yan jaridar basu ruwaito mafi akasarin kashe-kashen da ake yi.

Ya bayyana hakan a taron majalisar addinai na rubu'in karshen shekarar 2021, rahoton Tribune

Sultan Abubakar ya yi kira ga Musulmai da Kirista su daina jin tsoron barazanar yan bindiga.

Kara karanta wannan

Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin Musulmi ya yi tsokaci kan kisan matafiya a jihar Sokoto
Sarkin Musulmi ya yi tsokaci kan kisan matafiya a jihar Sokoto

Ya bayyana yadda wasu mutane ke aiko wasika a Zamfara cewa duk wanda aka kama yana zuwa Coci za'a kashe shi.

Yace:

"Lokacin da na ga takardar da yan bindiga ke yiwa Kiristoci barazana a Zamfara, sai nayi tambaya shin menene aikin jami'an tsaronmu."
"Ba zan daina zuwa Masallaci ba don wasu sun yi rubutu a takarda cewa idan na shiga Masallaci za'a kashe ni, su kasheni din, dama zan mutu, saboda haka Kiristoci su daina tsoron zuwa Coci saboda wasu na musu barazana."

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

Manyan mutanen garin Sabon Birni a karkashin kungiyar Gobir Development Association sun aikawa shugaba Muhammadu Buhari takarda.

Jaridar Daily Trust tace kungiyar Gobir Development Association ta sanar da mai girma shugaban kasa ne irin kisan kiyashin da ake yi wa mutanen Sabon Birni.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ba Zan Ajiye Aiki Ba Kan Yawaitar Tserewar Fursunoni Daga Gidan Yari, Ministan Buhari

A wasikar ta su, dattawan jihar sun bayyana cewa hankalinsu ya tashi, babu wani katabus a tare da su, bayan zaluncin da aka yi masu kamar dai yadda aka saba.

Da suke bayani a takardar a ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021, kungiyar tace yan bindiga sun addabi yankin Isa, Sabon Birni da Goronyo da bangaren Shinkafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel