Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa

Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa

  • Matasa sun fita zanga-zanga a titunan jihohin arewa da suka hada da Kano, Bauchi, Sokoto, Zamfara da Abuja.
  • Matasan sun nuna cewa ba za su amince da yadda rashin tsaro ke cigaba da wanzuwa ba a yankin suna kira ga Shugaba Buhari da gwamnoni su dauki mataki
  • A Jihar Kano, matasan sun yi tattaki daga sakatariya har zuwa gidan gwamnati inda jami'an tsaro suka tarbe su sannan suka saurare su

Matasa a halin yanzu sun fita titunan wasu garuruwa a arewacin Najeriya suna zanga-zanga kan yawaitar kashe-kashe a yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Duk da cewa a yanzu ana fama da matsalar rashin tsaro a sassan Najeriya da dama, yan ta'adda da yan bindiga sai kara kai hare-hare suke yi duk da kokarin da gwamnati ke yi na kawo karshen su.

Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa
Rashin Tsaro: Matasan Arewa sun yi zanga-zanga, sun bakaci Buhari da gwamnoni su samar da tsaro. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matasa sun yi zanga-zanga a Kano, Bauchi, Zamfara, Sokoto da Abuja

An hangi masu zanga-zangar dauke da takardu a jihohin Kano, Bauchi, Zamfara da Sokoto, rahoton Daily Trust.

An kuma hangi wasu masu zanga-zangar a babban birnin tarayya, Abuja.

Suna ta wake na zaman lafiya tare da kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi su kara kaimi don ganin sun magance matsalar rashin tsaron.

A Kano, matasa sun kama hanyar zuwa gidan gwamnati, dauke da takardu masu rubutun 'Zubar Da Jinin Ya Isa Haka.'

Zainab Naseer Ahmad, wacce ta jagoranci zanga-zangan na lumana, ta koka kan yadda kallubalen na tsaro ke barazana ga rayuwar yan Najeriya.

Kalamanta:

"Mun zo ne mu nuna damuwar mu tare da aika sako ga shugabannin mu; mun gaji da yadda batun tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.

"Yau da gobe, ana rasa rayuka, ana kashe mutane tamkar dabobi. Muna neman a dawo mana zaman lafiya a garuruwan mu.
"Abin da muke cewa shine, ya isa haka, zubar da jinin ya isa! Yaran da ba su zuwa makaranta suna karuwa, marayu ga su birjik a ko ina.
"Muna fargaban yin tafiya, tattalin arziki yana tabarbarewa. Ana kona matafiya."

Masu zanga-zangar sun yi tattaki daga sakatariyar Audu Bako zuwa Gidan Gwamnatin Kano, inda jami'an tsaro suka tarbe su, suka saurare su sannan suka yi alkawarin za su isar da sakonsu wurin da ya dace.

Yan Najeriya sun fusata sosai tun bayan rahoton yadda yan bindiga suka kona fasinjoji da ransu a Sokoto a farkon makon nan.

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

A wani labarin, Kwamishinan 'yan sandan Jihar Sokoto, CP Kamaludeen Okunola, ya tabbatar da cewa an kashe mutum 23 yayin harin da aka kai wa matafiya a Angwan Bawa a karamar hukumar Sabon Birni na Jihar.

Okunola, wanda ya tabbatar da adadin a jiya, bayan taron tsaro da Gwamna Aminu Tambuwal, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, ya kara da cewa an tura jami'ai su binciko wadanda suka aikata.

Kakakin yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar, ya bada labarin yadda yan bindigan suka kai wa motar da ke dauke da fasinjoji 42 hari, hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 18.

Asali: Legit.ng

Online view pixel