Hare-hare sun yawaita a Zamfara, tawaga ta tafi ganawa da kasurgumin dan bindiga

Hare-hare sun yawaita a Zamfara, tawaga ta tafi ganawa da kasurgumin dan bindiga

  • Yayin da hare-hare suka yawaita a jihar Zamfara, wasu mazauna sun dauki hanyar neman zaman lafiya da 'yan bindiga
  • An ce, wata tawaga ta hadu domin tattauna zaman lafiya da wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga, Turji
  • Har zuwa yanzu, ba a san sakamakon tattaunawar ba, amma dai an ce a baya Turji ya yi watsi da tawagar farko

Zamfara - Sakamakon hare-haren wuce gona da iri a yankin Shinkafi a jihar Zamfara, musamman kan matafiya dake kan hanyar da ta hada Gusau zuwa Sabon Birni, a jihar Sokoto, an aika da sabon jakada domin ganawa da kasurgumin dan bindiga, Turji.

A farkon watan Nuwamba, Turji ya yi watsi da tawagar Shinkafi ta neman tattaunawa, wadanda rahotanni suka ce sun je wurinsa domin neman zaman lafiya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Taswirar jihar Zamfara
Hare-hare sun yawaita a Zamfara, tawaga ta tafi ganawa da kasurgumin dan bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin garin Shinkafi, Alhaji Ali Mamman, ya ce an sha kai hare-hare a babbar hanyar tun bayan harin da sojoji suka kai ta sama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar iyaye da sauran ‘yan uwa na aminin Turji, Dan Bokkolo.

A baya an ruwaito yadda sojoji suka yi ruwan bama-bamai a maboyar ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An shafe kwanaki ana kai hare-haren, inda wani mazaunin garin ya shaida wa Daily Trust cewa ‘yan bindigar na kai hare-hare a wasu lokutan har sau uku a kullum.

Ya ce duk da haka mazauna yankin sun sami kwanciyar hankali bayan tura karin sojoji a ranar Litinin.

An gano cewa tawagar ta bar garin Shinkafi ne da yammacin ranar Litinin din da ta gabata don ganawar. Sai dai ba a san sakamako ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

Wata majiyar tsaro a Gusau ta ce:

“A cikin tawagar akwai mutanen sansanin Halilu. Ga dukkan alamu Halilu ya samu sauko don tattaunawa kuma da alama yana aiki tare da wasu jami’ai domin kawo wasu domin a tattauna."

'Yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue

A wani labarin, wasu 'yan bindiga sun bindige wani babban malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Benue da ke Ugbokolo a yammacin jiya Lahadi a sashin Eke na hanyar Otukpo zuwa Enugu a karamar hukumar Okkwu na jihar Benue.

Marigayin malamin, mai suna Adah Echobu Chris, wanda aka fi sani da, “The Bull”, an yi zargin wasu ‘yan bindiga ne suka kai masa hari a lokacin da yake komawa mazauninsa da ke Ugbokolo daga garin Eke, da ke yankin karkara.

Shaidu sun ce malamin yana tuka motarsa ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kama shi suka harbe shi har lahira.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Asali: Legit.ng

Online view pixel