Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

  • Rundunar Yan sandan Najeriya reshen Jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutum 23 a harin da 'yan bindiga suka kai wa matafiya
  • Yan sandan sun ce binciken da suka yi ya tabbatar da cewa fasinjoji tara cikin 30 da suke cikin motar sun tsira da ransu
  • Kakakin 'yan sandan ya ce kwamishina ya tura jami'ai zuwa wurin da abin ya faru domin kamo wadanda suka yi laifin su girbi abin da suka shuka

Sokoto - Kwamishinan 'yan sandan Jihar Sokoto, CP Kamaludeen Okunola, ya tabbatar da cewa an kashe mutum 23 yayin harin da aka kai wa matafiya a Angwan Bawa a karamar hukumar Sabon Birni na Jihar.

Okunola, wanda ya tabbatar da adadin a jiya, bayan taron tsaro da Gwamna Aminu Tambuwal, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, ya kara da cewa an tura jami'ai su binciko wadanda suka aikata.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto
'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Harin Da Ka Kaiwa Matfiya a Sokoto. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kakakin yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar, ya bada labarin yadda yan bindigan suka kai wa motar da ke dauke da fasinjoji 42 hari, hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 18.

Mutum tara cikin 30 sun tsira da ransu

Ya yi bayanin cewa sun tabbatar motar na dauke ne da fasinjoji 30, ya kara da cewa tara cikinsu ne suka tsira yayin da 21 suka kone kurmus.

Shaidan gani da ido ya tabbatarwa Guardian cewa yan bindigan sun harbi motar da ke dauke da fasinjojin ne kafin suka cinna mata wuta da fasinjojin a ciki.

Shugaba Buhari ya jajintawa iyalan wadanda suka rasu

Da ya ke martani kan lamarin, Shugaba Muhamadu Buhari ya nuna bakin cikinsa kan abin da ya kira 'mummunan hari kan matafiya da ba-su-ji-ba ba-su-gani ba a jihar Sokoto.'

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Hakazalika, Majalisar Dattawa ta Najeriya, ita ma ta yi jamamin rasuwar matafiyar, wadanda aka kona kurmus a hanyarsu na zuwa Gayan, Jihar Kaduna.

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel