Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun bi gida-gida a Abuja, sun kashe matan aure, sun sace mutane

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun bi gida-gida a Abuja, sun kashe matan aure, sun sace mutane

  • Wasu miyagun yan bindiga sun bi gida-gida, sun yi awon gaba mutane da dama a babban birnin tarayya Abuja
  • Rahoto ya bayyana cewa maharan sun harbe wata mata har Lahira, yayin da suka nemi mijinta ba su gani ba
  • Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru, yace maharan sun yi awon gaba da aƙalla mutum 8 a harin Talata da Laraba

Abuja - An bindige wata matan aure mai suna Salamtu har lahira yayin da yan bindiga suka farmaki yankin Piri, karamar hukumar Kwali dake Abuja.

Dailytrust ta ruwaito cewa akalla mazauna yankin mutum 8 maharan suka yi awon gaba da su a harin, wanda ya faru tsakanin ranakun Talata da Laraba.

Wani mazaunin yankin, Yakubu Saidu, yace maharan sun fara kutsawa cikin gidaje biyu, suka sace mutum biyu yayin da suka bude wuta.

Kara karanta wannan

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun bi gida-gida a Abuja, sun kashe matan aure, sun sace mutane Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yace masu garkuwan sun zo da nufin sace wani dilan motoci amma tun da ba su same shi ba, sai suka sace yan uwansa biyu ranar Talata da daddare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin sun kashe mutane ne?

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun sake dawowa yankin ranar Laraba lokacin da suka bindige Salamatu.

Matar, wacce ita ce uwar gidan Yusuf Maigunwa, wani babban dilan Doya a Kwali, ta yi kokarin tserewa ne ta kofar baya lokacin da suka harbe ta.

Yace:

"Mijin matar na cikin gida lokacin da yan bindigan suka shiga, amma ba su iya gano wurin da ya ɓuya ba, sai suka tasa matarsa ta biyu da wasu mutum biyu a gidan."

Mutumin ya kara da cewa sauran yan tawagar maharan, waɗan da suka tsaya a wurare daban-daban a yankin, sun kutsa gidaje biyu, sun sace mutum uku.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a

Yan sanda ba su ce komai ba

Kakakin rundunar yan sanda na babban brinin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, ba ta daga kiran waya ba, kazalika ba ta dawo da amsar sakon da aka tura mata ba dan jin ta bakin hukumar yan sanda.

A wani labarin na daban kuma Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi a jihar Zamfara

A cewar wasu mazauna yankin, yan bindigan sun ce zasu cigaba da kai hari kauyuka har sai gwamnati ta buɗe kasuwar dabbobi ta Shinkafi.

Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan wani harin sojin sama da ya hallaka iyalan Turji, yan bindigan dake karkashinsa suka cigaba da matsawa mutanen yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel