Tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari kan hanyar Kauran Namoda-Shinkafi, sun kone matafiya da ransu

Tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari kan hanyar Kauran Namoda-Shinkafi, sun kone matafiya da ransu

  • Yan ta'adda sun kai wani mummunan hari kan hanyar Kauran Namoda-Shinkafi a jihar Zamfara, sun sace mutane da dama
  • Rahoto ya nuna cewa yan bindigan karkashin jagorancin Turji, sun mamaye hanyar, inda suka kashe mutane 6
  • a cewar wasu mazauna yankin, yan bindigan sun ce zasu cigaba da kai hari kauyuka har sai gwamnati ta buɗe kasuwar dabbobi ta Shinkafi

Zamfara - Yan bindiga sun kashe mutum 6, sannan sun tasa keyar wasu da dama yayin da suka farmaki matafiya akan hanyar Kauran Namoda-Shinkafi a jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin da lamarin ya shafa ya shaidawa wakilin Dailytrust cewa yan ta'addan sun kone wasu daga cikin motoci da mutanen dake ciki, ta yadda ba zaa iya gane gawarwakin ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue

Jihar Zamfara
Tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari kan hanyar Kauran Namoda-Shinkafi, sun kone matafiya da ransu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan bindigan bisa jagorancin Turji, sun ƙara matsa lamba wajen kai hare-hare hanyar Shinkafi-Kauran Namoda bayan luguden wutan sojin sama ya hallaka gwaggwon Turji, mijinta, da yan ta'adda da dama.

Premium times ta rahoto Mutumin yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yan bindigan sun rufe kan hanyar a tsakanin Kwanar Jangeru da Moriki kuma tuni matafiya suka dena bin hanyar domin kare rayuwarsu.
"Ba wanda ya isa yaje ɗakko gawar mutanen da suka kashe. Luguden wuta da sojojin sama suka yi a kansu, shine ya fusata su a yanzu. Harin sojin ya taba sansanin Turji kuma wasu daga cikin iyalansa sun bakunci lahira."

Yan bindiga na neman a bude kasuwar dabbobi a Zamfara

Haka nan kuma wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun tsananta hare-hare kan mutane ne domin nuna adawarsu da ɗaukar dogon lokaci ba'a bude kasuwar dabbobi ta Shinkafi ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50

Mun ji wasu daga cikin yan bindigan na cewa zasu cigaba da tsananta kai hari Ƙauyuka, kuma suna sace matafiya har sai an bude kasuwar, inji mazauna yankin.

Yayinda muka nemi jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, yace, "Ku bani wani ɗan lokaci zan neme ku."

A wani labarin kuma Iyayen Ango da Yan uwansa sun mutu awanni kadan bayan kammala daura aure

Bikin aure wani sha'ani ne dake kawo murna da farin ciki musamman ga ma'aurata da kuma yan uwan su na jini.

Wani hatsarin mota a Bayelsa ya lakume rayukan iyaye da yan uwan wani Ango, a kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin ɗaura aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel