Da Dumi-Dumi: Saudiyya ta dakatar da Jiragen Najeriya shiga ƙasar saboda Omicron

Da Dumi-Dumi: Saudiyya ta dakatar da Jiragen Najeriya shiga ƙasar saboda Omicron

  • Saudiyya ta dakatar da jirage shiga kasar daga Najeriya saboda dakile yaɗuwar sabon nau'in cutar COVID19 na Omicron
  • Wani jami'in ofishin jakadancin Saudiyya a Kano yace sun samu umarnin hana jirage tashi domin zuwa Saudiyya
  • Sai dai wani babban ma'aikacin kamfanin jiragen sama yace ba zai tabbatar ba saboda wasu jirage biyu sun nufi Jidda yau da safe

Kano - Masarautar Saudiyya ta dakatar da zirga-zirgan jiragen sama daga Najeriya saboda kokarin dakile yaɗuwar sabon nau'in cutar Omicron.

Dailytrust ta rahoto cewa a ranar Laraba wani labari mara tabbas ya nuna cewa masarautar na shirin tattaro wasu yan Najeriya da suka shiga ƙasar zuwa gida kan Omicron.

Wasu majiyoyi a ofishin jakadancin Saudiyya da kuma ma'aikata a filin jirgin Malam Aminu Kano sun tabbatar da cewa an umarci su dakatar da jiragen dake shirin shiga Saudiyya kan Omicron.

Kara karanta wannan

Amarya ta yiwa Angonta kyautan jirgin ruwa mai tsada ranar daurin aurensu

Saudiyya
Da Dumi-Dumi: Saudiyya ta dakatar da Jiragen Najeriya shiga ƙasar saboda Omicron Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan ɗage dokar hanin a kan Najeriya, mutane da dama sun ziyarci kasar domin gudanar da aikin Umrah, musamman daga jihar Kano.

Ma'aikata sun tabbatar

Wani jami'in ofishin jakadancin Saudiyya a Kano, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa sun samu umarnin su dakatar da jirage zuwa kasar daga Najeriya sabida dakile yaɗuwar sabon nau'in korona na Omicron.

Haka nan kuma wani ma'aikaci a filin jirgin Kano yace tuni aka soke jadawalin jiragen da zasu ɗibi mutane zuwa aikin Umrah a Saudiyya saboda dokar.

Vanguard ta rahoto Yace:

"Eh dagaske ne, domin an soke jadawalin jiragen da zasu kai masu aikin Umrah kuma ba maganar cigaba da zirga-zirgan jirage zuwa kasar har sai sanarwa ta gaba."
"Ina tunanin suna koyi da matakan da sauran ƙasashe suka ɗauka kamar Birtaniya a kokarin su na dakile shigar cutar ƙasar."

Kara karanta wannan

Ba zan sake Zina ba sai Allah ya bani miji, Jarumar Nollywood

Sai dai wani babban jami'in kamfanin jiragen sama yace ba zai iya tabbatar da lamarin ba domin jirage biyu, Qatar da Badar Air, sun bar Abuja zuwa Jiddah da Safiyar Laraba.

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da hana jiragen Najeriya shiga kasashen Birtaniya da Kanada kan Omicron.

A wani labarin na daban kuma Jirgin yakin NAF ya yi ruwan bama- bamai kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja

Rahoto ya bayyana cewa yayin harin, jirgin sojojin saman ya sheke yan bindiga akalla 45 sannan kuma ya lalata ma'adanar makaman su.

Yan bindigan na amfani da wannan wurin a matsayin maɓoyarsu, da kuma kaddamar da hari kan matafiya a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel