Ba zan sake Zina ba sai Allah ya bani miji, Jarumar Nollywood

Ba zan sake Zina ba sai Allah ya bani miji, Jarumar Nollywood

  • Yar wasar kwaikwayon ta bayyana cewa duk zinace-zinacen da tayi rayuwarta bai amfaneta da komai ba
  • Jarumar ta bayyana cewa yanzu ta koma ga Allah kuma zata kame kanta har zuwa lokacin ta samu miji

Jarumar wasan kwaikwayon Nolywood, Sylvia Ukaatu, ta lashi takobin komawa ga Allah har zuwa lokacin da zata samu mijin aure.

Sylvia Ukaatu ta bayyana hakan ne a hirar da tayi kwanakin nan kuma Allure Vanguard ta ruwaito.

Ta yi nadamar biyayya wa Shaidan da tayi shekarun baya kuma yanzu ta shirya tuba da komawa ga Allah.

Tace:

"Na koma ga Allah. Ba zan sake fifita kudi kan tsoron Allah ba. Dukkan shekarun nan ba tare da biyayya ga Allah ba sun zama aikin banza, shi yasa nayi alkawarin cewa ba zan sake jima'i ba sai na yi aure."

Kara karanta wannan

Na gida ya kashe Dakta Nasir Rabe, Kwamishanan Kimiyar Katsina: Gwamna Masari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina addu'a wannan sabon matsaya da na dauka zai wanke min zunubai na lokacin da nike bin shaidan."

Ba zan sake jima'i ba sai Allah ya bani miji, Jarumar Nollywood
Ba zan sake jima'i ba sai Allah ya bani miji, Jarumar Nollywood Hoto: allure.vanguardngr.com
Asali: UGC

'Yar jihar Anambra wacce a baya ta bayyana yadda take son jima'i sosai a baya kuma ta yi zina da mutane daban-daban.

A cewarta:

"Na kasance mai son jima'i sosai kuma na yi zinace-zinace saboda lokacin rayuwata nike ci....Lokaci ya yi da zan koma ga mahalicci na. Idan lokaci yayi zai bani masoyi na."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel