Bamu taba kwanciyar aure dashi ba, amma 'ya'yanmu hudu, inji tsohuwar matar Fani-Kayode

Bamu taba kwanciyar aure dashi ba, amma 'ya'yanmu hudu, inji tsohuwar matar Fani-Kayode

  • Tsohuwar sarauniyar kyau Precious Chikwendu da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode sun sha martani daga 'yan Najeriya kan batun aurensu
  • Chikwendu ta zargi dan siyasar da cin zarafinta sau da yawa tare da umurtar masu tsaronsa da su kulle ta
  • Chikwendu, mahaifiyar ‘ya’ya hudu ta kuma zargi Fani-Kayode da cin amanarta, inda ta bayyana cewa ya rike aurensa da matarsa ta uku kuma suna tare

Jaruma Precious Chikwendu ta roki kotu da ta ba ta cikakkiyar damar kula da ‘ya’yanta da ta haifa tare da Femi Fani-Kayode.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa tsohuwar sarauniyar kyau din ta ce ta haifi ’ya’yanta ne ta hanyar yi mata dashen 'ya'ya a kimiyyance yayin da aka tilasta mat zaman aure dashi.

Kara karanta wannan

'Yan IPOB sun dasa bama-bamai, sojoji sun fatattakesu sun kwace tarin makamai

Fani-Kayode da Tsohuwar matarsa
Bamu taba kwanciyar aure dashi ba, amma 'ya'yanmu hudu, inji matar Fani-Kayode | @snowhiteey, @real_ffk
Asali: Instagram

Chikwendu ta bayyana cewa bata taba kasancewa a zaman aure da Fani-Kayode ba saboda bai biya kudin aurenta ba.

Tsohuwar sarauniyar kyawun ta bayyana cewa aurenta da Fani-Kayode yana cike da bala'i, tashin hankali a cikin gida, wulakanci a idan duniya, da rashin kusantar juna saboda rashin iya tabuka komai a jima'i da dai sauran matsaloli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Chikwendu uwar ‘ya’ya hudu, ba za ta iya sake zama da dan siyasar ba. Daga nan sai ta bukaci a mayar mata da kadarorinta da ke gidan Fani-Kayode.

Martanin 'yan Najeriya

Lokacin da aka yada batun a kafar Instagram, 'yan Najeriya sun fadi ra'ayoyinsu mabanbanta.

anniesbedring:

"Haaaaa shekara 6? Kin yi kokari oh."

fashiondoctor19:

"Gaskiya wannan mutumin ya azabtar da wannan baiwar Allah, ina addu'ar ta gaggauta kubuta daga munanan ayyukansa."

Kara karanta wannan

Abokan aiki na dariya suka rika min: Matar da ta ajiye aikin ɗan sanda ta rungumi noma

ebaycarder:

"Kyautar Karya Ta Shekara Ta Tafi Ga........."

kolawokola123:

"Omoo ba mamaki kullum yana cikin fushi.. Baba abu ba ya aiki.. Ina so in bashi hakuri akan rashin jin zafinsa."

greatzhair1:

"Na yarda da ita saboda yadda mutumin nan yake fadawa soyayya a cikin mintuna 2 akwai alamar tambaya."

thereal.amaka:

"Kamar dai FFK bai hadu da sa'arsa ba."

iamrealebere:

"Na yarda da ita, lokacin da mutum yake son jan gwanda iri daban-daban, tabbas ba za a sanya *** a wuri guda ba."

Tsohuwar Matar Fani-Kayode ta kai shi kotu, tana neman ya biya ta Naira Miliyan 800

A wani labarin, Precious Chikwendu wanda aka fi sani da Snow White, ta kai karar tsohon mai gidanta, Femi Fani-Kayode, a wani babban kotun tarayya a Abuja.

Jaridar Punch tace Miss Precious Chikwendu tana neman kotun tarayyar ta biya mata hakkinta.

Precious Chikwendu ta kai karar Femi Fani-Kayode, Sufeta-Janar da sauran jami’an ‘yan sanda, tana neman a biya ta Naira miliyan 800 domin ta rage zafi.

Kara karanta wannan

Matar aure ta yiwa budurwar mijinta wanka da fetur sannan ta banka mata wuta har lahira

Asali: Legit.ng

Online view pixel