Tsohuwar Matar Fani-Kayode ta kai shi kotu, tana neman ya biya ta Naira Miliyan 800

Tsohuwar Matar Fani-Kayode ta kai shi kotu, tana neman ya biya ta Naira Miliyan 800

  • Precious Chikwendu ta je kotu tana karar tsohon mijinta, Femi Fani-Kayode
  • Chikwendu ta hada da IGP da wasu jami’an ‘yan sanda a karar da ta shigar
  • Bazawarar ‘dan siyasar ta bukaci kotun tarayyar ya sa a biya ta miliyan 800

Abuja - Precious Chikwendu wanda aka fi sani da Snow White, ta kai karar tsohon mai gidanta, Femi Fani-Kayode, a wani babban kotun tarayya a Abuja.

Jaridar Punch tace Miss Precious Chikwendu tana neman kotun tarayyar ta biya mata hakkinta.

Precious Chikwendu ta kai karar Femi Fani-Kayode, Sufeta-Janar da sauran jami’an ‘yan sanda, tana neman a biya ta Naira miliyan 800 domin ta rage zafi.

Sauran wadanda aka yi kara a babban kotun tarayyar sune Mataimakin Sufeta-Janar na sashen CID, kwamishinan ‘yan sanda na Abuja, CSP James Idachaba.

Kara karanta wannan

MURIC ta mayar da martani kan sauya shekar Fani-Kayode zuwa APC, ta bayyana abin da zai faru

Wanda ta kai karar tace ta na bukatar a biya ta wadannan kudi ne domin jami’an ‘yan sandan sun ci zarafin ta a lokacin da take tsare a hannun jami’an tsaro.

Tsohuwar Matar Fani-Kayode
Precious Chikwendu da Femi Fani Kayode Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abdul-Aziz Jimoh ya tsaya wa Chikwendu

Rahoton yace Chikwendu ta shigar da karar ta hannun wani lauyanta, Abdul-Aziz Jimoh, wanda ya bukaci kotu ta haramta wa IGP da rundunarsa taba matar.

Chikwendu tana so ‘yan sanda su daina matsa mata lamba har zuwa lokacin da za a kammala shari’a tsakaninta da Fani-Kayode kan wanda zai rike ‘ya ‘ya.

Tsohon Ministan tarayya, Fani-Kayode ya taba auren Precious Chikwendu wanda ta haifa masa yara hudu, wanda yanzu ake rigimar wanene zai zauna da su.

Har ila yau, Precious Chikwendu tana so Alkali ya zartar da cewa babu wanda ya isa ya tursasa mata zuwa wajen ‘yan sanda domin amsa zargin da ke kanta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri

Aikin Siemens ya tsaya

Kun ji labari cewa shekaru biyu da gwamnatin tarayya da kamfanin Siemens suka sa hannu a yarjejeniyar wutar lantarki, har yanzu ba a fara yin aikin ba.

Binciken da aka yi ya nuna cewa aikin Presidential Power Initiative (PPI) da ake sa rai zai samar da megawatt 25, 000 na karfin wuta bai kankama ba har yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng