'Yan IPOB sun dasa bama-bamai, sojoji sun fatattakesu sun kwace tarin makamai

'Yan IPOB sun dasa bama-bamai, sojoji sun fatattakesu sun kwace tarin makamai

  • Jami'an sojin Najeriya ta fatattaki wasu mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB a wani yankin jihar Imo
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, jami'an tsaron sun kuma kwato wasu bama-bamai duk daga 'yan IPOB
  • Hakazalika, rundunar ta bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankali kuma su ci gaba da bin doka da oda suyi watsi da IPOB

Imo - A ranar Litinin ne sojoji suka dakile wani yunkuri da wasu ‘yan haramtacciyar kungiyar IPOB) da mambobinta na ESN suka yi na kai hare-hare kan wasu al’ummomi biyu a jihar Imo.

Haramtacciyar kungiyar IPOB/ESN tayi yunkurin tayar da kayar baya a kan al’ummar Mgbidi da Awo-Mmamma da ke cikin karamar hukumar Oru ta Yamma a Imo, inda sojojin rundunar Golden Dawn suka fatattakesu.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya ba manema labarai ranar Litinin a Enugu, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fashewar bama-bamai a Maiduguri: Rundunar soji ta magantu, ta ce a kwantar da hankali

Mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB/ESN
'Yan IPOB sun dasa bama-bamai, sojoji sun fatattakesu sun kwace tarin makamai | saharareporters.com
Asali: UGC

Mista Nwachukwu ya ce kungiyar ta nufi barna kan mutanen al’ummomin biyu ne saboda kin bin haramtaccen umarninta na “zama-a-gida” a ranar Litinin, 6 ga Disamba.

A cewarsa:

“Martanin gaggawa da sojoji suka yi ya tilasta wa maharan, a kan motoci Sienna biyu da wata mota kirar Toyota Hilux su yi watsi da barnarsu, su kuma janye cikin rudani.

"A halin yanzu sojoji suna kan hanyar tarfa 'yan ta'addan."

Kakakin rundunar ya ce a wani labarin kuma, sojojin sun gano wasu bama-bamai guda hudu da ‘yan kungiyar IPOB/ESN suka binne a hanyar Orlu zuwa Owerri, kamar yadda Punch ta rahoto.
“Dakarun ’yan banga, wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mgbidi/Awo-mmama sun gano bama-baman da aka dasa a nesa da tazarar mitoci 15 a bangarori biyu na titin kuma suka kwance su lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan PDP sun shigo jam'iyyarmu suna bata mana harkoki, inji sabon kwamitin APC

“Ba a samu asarar rai ba yayin kwancewar.
“Sojojin sun kuma samu nasarar kwato wasu bama-bamai guda hudu da ba su fashe ba, baturin babur daya, na’urorin ankarar da ababen hawa, wani nau'in bam daya, wayoyi da batura.

Ya kara da cewa:

"An bude hanyar lafiya kuma masu ababen hawa sun ci gaba da bin hanyar."

Mista Nwachukwu ya bukaci duk ‘yan yankin masu bin doka da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum tare da yin watsi da dokar “zama-a-gida” ta haramtacciyar kungiyar.

Ya kara da cewa:

"Muna kira ga mutanen kirki na Mgbidi, Awo-Mmama da Omuma da su kai rahoton duk wani da ake zargin dan kungiyar ne, wanda zai iya neman mafaka don gujewa hukumomin tsaro da suka dace."

Fashewar bama-bamai a Maiduguri: Rundunar soji ta magantu, ta ce a kwantar da hankali

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya a ranar Asabar ta kawar da fargabar mazauna Maiduguri, biyo bayan fashe-fashen da suka faru a wasu al’ummomi a babban birnin na jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke dan IPOB yayin da tsagerun ke kokarin sace likitoci a jihar Imo

Rahotanni sun bayyana yadda karar fashewar wasu abubuwa a unguwar Gomari da jerangiyar gidaje na 1000 a Maiduguri da sanyin safiyar Asabar ta haifar da tashin hankali.

Da take mayar da martani kan lamarin, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu 'yan ta'adda na Boko Haram ne da kuma 'yan kungiyar ISWAP suka yi ta harbe-harbe a cikin wadannan yankuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel