Matar aure ta yiwa budurwar mijinta wanka da fetur sannan ta banka mata wuta har lahira

Matar aure ta yiwa budurwar mijinta wanka da fetur sannan ta banka mata wuta har lahira

  • Matar aure ta rabu da mijinta ta koma zama da wani magidanci babu aure tsakaninsu, gashi matar magidancin ta babbaka ta
  • Matar wanda ta koma zama wajensa ta yi mata wanka da man fetur kuma ta cinna mata ashana
  • Ana jinyanta a asibiti amma bayan dan lokaci tace ga garinku

Ota - Wata matar aure mai 'yaya uku a jihar Ogun, Kehinde, ta yiwa budurwar mijinta wanka da man fetur sannan ta cinna mata wuta kuma hakan yayi sanadiyar mutuwarta.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ta tabbatar da labarin inda tace tuni an damketa, rahoton DailyTrust.

A cewar yar sandar, sun damke matar ne bayan tsohon mijin matar aka kona mai suna Fatai Olugbade ya karar hedkwatansu dake Ota.

Fatai ya bayyanawa yan sanda cewa tuni sun rabu kuma ta koma soyayya da wani.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta sako faston da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai

Matar aure ta yiwa budurwar mijinta wanka da fetur sannan ta banka mata wuta har lahira
Matar aure ta yiwa budurwar mijinta wanka da fetur sannan ta banka mata wuta har lahira
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Ina zargin tana hulda da wani kwarto masu suna Ismail Wasiu, sai na tambayeta gaskiyar lamarin, amma abin mamaki shine, ta kwashe kayanta ta koma gidan kwarton."
"A ranar 14 ga Nuwamba, sai rikici ya barketa tsakaninta da matar Wasiu, kawai sai matar tayi mata wanka da Fetur ta cinna mata wuta."
"Yan uwanta sun garzaya da ita asibiti amma ta mutu daga baya."

Kaakin yan sandan ya bayyana cewa tuni suke nemi matar Wasiu kuma suka damketa.

"Yayin bincike, ta amsa laifin amma tace bata san abinda ya kaita yin haka ba,"

Asali: Legit.ng

Online view pixel