Abokan aiki na dariya suka rika min: Matar da ta ajiye aikin ɗan sanda ta rungumi noma

Abokan aiki na dariya suka rika min: Matar da ta ajiye aikin ɗan sanda ta rungumi noma

  • Bayan sakin aikinta na hukumar ‘yan sanda, Vemuhle Thisila ta koma kiwon kaji tare da sayar dasu don yin hidimomin rayuwarta
  • Ta bayyana yadda abokan aikinta su ka dinga yi mata dariya tare da zundenta a lokacin da ta bayyana kudirinta na sakin aikin
  • Yanzu haka Thisila ta koma harkar kiwon shanu da kaji kuma tana matukar alfaharin daukar wannan babban matakin a rayuwarta

Afirka Ta Kudu - Labarin Vamuhle Thisila ya na daya daga cikin labarai masu ban al’ajabi da nuna amfanin jajircewa da dagewa a rayuwa.

Tsohuwar ma’aikaciyar ‘yan sandan ta bar aikinta saboda damuwar da ta ke fuskanta a lokacin don ta koma harkar kiwon kaji.

Yanzu haka tana kiwon shanu tare da kaji a wani katafaren gidan gona, kamar yadda Black Capitalist ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Annobar da ta fi Koronar farko na tunkaro duniya, kowa ya shirya inji masana

Thisila ta ce bata yi dana sanin sakin aikinta ba a matsayin ma’aikaciyar hukumar ‘yan sanda.

Abokan aiki na dariya suka rika min: Matar da ta ajiye aikin dan sanda ta rungumi noma
Budurwa ta ajiye aikin dan sanda, yanzu kaji ta ke sayarwa. Hoto: Black Capitalist
Asali: UGC

Ta bayyana cewa abokan aikinta na baya sun dinga yi mata dariya akan yadda ta saki aikinta na dindindin ta koma kiwon kaji.

Duk da kalubalen da ta dinga fuskanta, hakan bai dameta ba don tasan burinta da take son ya cika.

Kamar yadda ta ce:

“Yanzu ina ciyar da kasar nan. Ina da isasshen wurin da zan cika buri na, kuma ina fatan cika burina. Yanzu haka burina ya kusa cika. Ina alfahari da zama manomiya.”

Legit.ng ta yi karo da labarin Thisila mai amfanarwa ne don haka ta wallafa a Facebook.

Ga wasu daga cikin tsokacin da mutane su ka dinga yi karkashin wallafar:

Kara karanta wannan

Ana wata: Shehin malami ya magantu, ya ce mata su daina yiwa mazajensu girki da aikin gida

Mpho Leballo ta ce:

“Ta burge ni da ta bar aikinta don cika burinta.”

Gcobani Manyakanyaka ta ce:

“Labari mai ban sha’awa.”

Ngqulunga Tee Tee ya rubuta:

“Na sara miki...”

Marie Rheeder ta rubuta:

“Kinyi kokari gaskiya.”

Thedis Tefo ya ce:

“Buri mai kyau, barka.”

Bidiyon Ƙasaitattun Kayan Alatu Da Matashi Ya Saka a Gidansa Na Kasa, Ciki Har Da AC, Babban TV Da Kujeru

Hausawa su kan ce hangen dala ba shiga birni ba, tabbas batun haka yake bayan bayyanar bidiyon tarin kayan alatun da wani mutum ya zuba wa gidansa na kasa a kafafen sada zumunta.

Kamar yadda ake ganin sauran gine-gine na kasa a kauyaku, haka gidan yake, sai dai idan aka duba cikinsa abin ba a cewa komai don ya hadu iya haduwa.

A falon gidan wani mutum na kasa har da na’urar sanyaya wuri ta AC, sannan wasu luntsuma-luntsuman kujeru na kece raina tare da fenti na gani da fadi.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Yadda wata mahaifiya ta sadaukar da rayuwarta domin ɗanta ya tsira

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel