Tashin Hankali: Iyayen Ango da Yan uwansa sun mutu awanni kadan bayan kammala daura aure

Tashin Hankali: Iyayen Ango da Yan uwansa sun mutu awanni kadan bayan kammala daura aure

  • Bikin aure wani sha'ani ne dake kawo murna da farin ciki musamman ga ma'aurata da kuma yan uwan su na jini
  • Wani hatsarin mota a Bayelsa ya lakume rayukan iyaye da yan uwan wani Ango, a kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin ɗaura aure
  • Jami'an hukumar FRSC da kuma yan sanda na cigaba da aikin bincike kan lamarin hatsarin

Bayelsa - Iyalan wani sabon ango a Bayelsa, sun shiga tashin hankali da jimami, biyo bayan mutum 9, ciki harda iyaye da yan uwan Angon, sun rasa rayukansu a mummunan hatsarin mota.

Dailytrust tace lamarin ya faru a Tollgate dake gaban Glory Land drive a kan hanyar Igbogene, Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Wani shaidan gani da ido, yace mutanen suna kan hanyar komawa gida a ƙaramar hukumar Sagbama bayan halartar ɗaura auren, yayin da lamarin mara daɗi ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

Hatsarin mota
Tashin Hankali: Iyayen Ango da Yan uwansa sun mutu awanni kadan bayan kammala daura aure Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotannin da muka samu sun bayyana cewa motar Bas ɗin da yan ɗaura auren suka shigo ta yi taho mugama da wata mota da ta fito daga Warri, jihar Delta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

FRSC sun kai ɗauki cikin lokaci

Jami'in hukumar kare haɗurra (FRSC) ya shaidawa manema labarai a wurin da hatsarin ya faru cewa sun yi gaggawar kai mutum hudu asibiti, amma ɗaya daga ciki ya mutu.

Ya kuma kara da cewa hukumarsu zata fitar da jawabi a hukumance kan lamarin amma a halin yanzun suna cigaba da bincike.

Yan sanda sun ɗauki mataki

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, yace hukumar yan sanda ta fara bincike kan ainihin abinda ya faru.

Tribune Online ta rahoto yace:

"Lamarin mara daɗi ya auku ne ranar 4 ga watan Disamba, 2021 da misalin karfe 5:00 na yamma a gaban Glory Land drive, Igbogene, kuma ya shafi motoci biyu; Bas kirar Toyota mai lamba AKL 652 YP, da kuma wata Jeep mai lamba KMK 923 AA."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Rikici ya barke, yan Acaba sun lakadawa yan sanda dukan tsiya a Legas

"Mun ɗauki zanen wurin da hatsarin ya faru kuma an ɗauke motocin daga wurin zuwa caji ofis ɗin Igbogene domin cigaba da bincike."
"Hakanan kuma jami'ai sun kai gawarwakin waɗan da suka mutu Asibitin koyarwa na jami'ar Neja Delta, yayin da waɗan da suka jikkata ke cigaba da jinya a nan asibitin."

A wani labarin kuma Bayan hatsarin kwalekwale da ya faru a Kano, Gwamnatin Ganduje ta dakatar da sufurin jiragen ruwa a Bagwai

Gwamnatin Kano ta sanar da ɗaukar matakin dakatar da sufurin jiragen ruwa a yankin karamar hukumar Bagwai.

Rahoto ya nuna cewa a zaman majalisar zartarwa, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai binciko musabbabin hatsarin da ya lakume sama da rai 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel