Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50

Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50

  • Bayan komawa garkuwa da mutane hanyar Kaduna/Abuja, yan bindiga sun shiga karamar hukumar Chikun
  • Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa ba'a taba kai hari irin wannan karamar hukumar ba sai yanzu
  • Duk da cewa gwamnati bata tabbatar da adadin wadanda aka sace ba, mutan gari sunce an kwashe akalla 50

Chikun - Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da mutane 50 yayinda yan bindiga suka kai hari Unguwar Gimbiya dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Wani mai idon shaida wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa wannan hari ya auku ne da sanyin safiyar Juma'a, 3 ga Disamba, 2021.

A cewarsa yan bindigan sun kai gari gidaje akalla 13 kuma sai da suka kwashe sa'o'i biyu suna diban jama'a.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu

Yace:

"Sun kai garmaki Ungwan Gimbiya dake Sabo, karamar hukumar Chikun dake Kaduna, sun kashe mutum 2, sun sace 50."

Yan bindiga kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50
Da duminsa: Yan bindiga kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50 Hoto: Samuel Aruwan
Asali: Facebook

Wani mazaunin daban, Gideon Jatau, a cewar Daily Trust, yace ba'a taba kai hari irin wannan ba a garin.

Yace suna fuskantar lamarin sace-sacen mutane amma wannan ya yi munin gaske.

Yunkurin samun karin bayanai daga bakin Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ci tura.

Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu

A wani labarin kuwa, babban jami'in dan sanda kuma DPO na garin Fugar, karamar hukumar Etsako Central a jihar Edo, CSP Ibrahim Ishaq, ya shaki kamshin yanci bayan kimanin mako guda hannun yan bindiga.

Kara karanta wannan

Matashin zai auri mata biyu rana guda bayan dirka musu ciki

Rahotanni sun nuna cewa an saki DPOn ne da daren Alhamis, 2 ga Disamba, 2021.

Kakakin yan sandan jihar Edo, Bello Kongtons, ya tabbatar da sakin DPOn amma bai yi tsokaci kan ko an biya kudin fansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel