Da Dumi-Dumi: Zamu ɗauki mataki kan FG cikin awanni 48, ASUU

Da Dumi-Dumi: Zamu ɗauki mataki kan FG cikin awanni 48, ASUU

  • Kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta bayyana cewa zata bayyana matakin da zata ɗauka nan da awanni 48
  • Gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawurran da ta ɗaukarwa ASUU, har wa'adin mako uku ya ƙare
  • Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Osodeke, yace ba su da wani zaɓi da ya wuce zartar da abinda mambobi suka bukaci kungiya ta yi

Abuja - Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa, ASUU, ta bayyana cewa zata ɗauki mataki kan gazawar gwamnatin tarayya wajen cika mata bukatunta, cikin awanni 48.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, shine ya bayyana haka a wata fira da jaridar Dailytrust ta wayar salula.

Shugaban ƙungiyar malaman yace ASUU zata kammala jin ta bakin kowane reshenta dake faɗin kasar nan, kuma daga nan zata bayyana mataki na gaba.

Kara karanta wannan

2023: Kotu zata yanke hukunci kan ko Atiku ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa

Osodeke da Buhari
Da Dumi-Dumi: Zamu ɗauki mataki kan FG cikin awanni 48, ASUU Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

ASUU ta gana da ministan kwadugo, Chris Ngige, wanda yake shiga tsakanin kungiyar da ma'aikatar ilimi, a ranar 14 ga watan Oktoba, kan batutuwa da dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene bukatun ASUU?

Daga cikin abubuwan da ɓangarorin biyu suka tattauna akai akwai; Ware kuɗaɗem ƙara habbaka jami'o'in gwamnati, alawus ɗin malaman jami'o'i, da alawus ɗin albashi na ƙarin girma.

Sauran sun haɗa da, cigaba da zama domin tattaunawa kan yarjejeniyar ASUU-FGN ta shekarar 2009, da kuma abinda ya shafi tsarin biyan albashi na IPPIS.

Gwamnatin tarayya ta ɗauki alkawarin biyan kudin alawus da suka kai biliyan N22.1bn da kuma wasu biliyan N30bn na gyaran jami'o'i.

Sai dai a ranar 15 ga watan Nuwamba, kungiyar malaman ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin makonni uku ta cika alƙawuran da ta ɗauka.

A cewar ASUU, matukar FG ta gaza cika waɗan nan alƙawurran, to ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta tsunduma yajin aiki.

Kara karanta wannan

Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da ɗalibansa mata

Ko wane mataki ASUU zata ɗauka yanzu?

Da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin, shugaban ASUU yace:

"Tun da gwamnati ta gaza cika mana bukatunmu, zamu bi matakan da ya dace. Zamu tuntubi kowane reshe sannan mu sanar da matakin da zamu ɗauka gobe."
"Wa'adin da muka ɗiba ya cika, zamu koma ga mambobin mu, duk abinda suka ce mu yi, bamu da zaɓi."

Da muka nemi jin ta bakin kakakin ma'aikatar kwadugo, Charles Akpan, ya umarci muje ma'aikatar ilimi da kuma ma'aikatar kudi su yi bayani kan dalilin jan kafa wajen biya wa ASUU bukatunta.

A wani labarin kuma NNPC ya bayyana cewa a watan Satumba, Najeriya ba ta samu ko sisi ba daga kudin ɗanyen man da ta fitar

A rahoton da kamfanin ya saka a shafin yanar gizo, NNPC ya bayyana cewa duk da hako ɗanyen mai sama da ganga miliyan daya a rana, babu wanda ya siya.

Kara karanta wannan

Najeriya ba ta samu ko sisi ba daga ɗanyen man fetur a watan Satumba, inji NNPC

Shekaru da dama da suka shuɗe, kasashen Indiya, China, da kuma kasar Amurka, sune suka kasance masu siyan ɗanyen mai da Najeriya ke samarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel