Labarin wani dan crypto: Cikin mintuna 5 na tsiyace daga miloniyan dan crypto

Labarin wani dan crypto: Cikin mintuna 5 na tsiyace daga miloniyan dan crypto

  • Wani dan kasuwar crypto ya fadi yadda ya kamo hanyar zama hamshakin attajiri a duniyar crypto - amma cikin minti biyar labari ya sauya
  • Ya ce ya yi asarar komai lokacin da kudin ya fadi kuma kafin ya ankara asusunsa ya koma $0, lamarin da dama yayi hasashe tun farko
  • Ya kuma bayyana cewa ba zai iya fita waje ba saboda tsoron kada a yi masa dariya domin an gargade shi kan tsoma kudinsa a tsabar crypto ta SQUID

Wani dan crypto ya ba da labarin yadda ya tsiyace a cikin kasa da mintuna 5 yayin da yake gab da zama miloniya.

Ta hanyar amfani da shahararriyar kafar yanar gizo ta Reddit mutumin ya yi ikirarin cewa ya tara dala miliyan 1.3 (N532.97 biliyan) yayin da ya sayi tsabar crypto ta SQUID wacce aka kirkira daga sunan wani fim din kafar fina-finai ta Netflix wato Squid Game.

Kara karanta wannan

A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami

Tsabar crypto ta SQUID
Labarin wani dan crypto: Cikin mintuna 5 na tsiyace daga miloniyan dan crypto | coinmarketcap
Asali: Facebook

Bayan ganin darajarsa ta haura sama da dala miliyan 2, kamar walkiya darajar kudin ta ragu zuwa $0.

SQUID, a watan Oktoba ya haura zuwa kololuwar farashin $2,681 kafin ya fadi zuwa $0.01 - faduwar 99.99% cikin kasa da wata guda.

Sukar darajar SQUID
Labarin wani dan crypto: Cikin mintuna 5 na tsiyace daga miloniyan dan crypto | Sun
Asali: Facebook

Akwai rahotanni da yawa da ke cewa SQUID na iya zama tsabar da 'yan damfara suka kirkira da aka fi sani da "rug pull" wanda ke faruwa lokacin da masu kirkiro sabbin tsabobin crypto suka zare wata tsabar crypto zuwa kudin gaske.

Mutumin ya ce ya yi "sha'awa" kuma yana son saka hannun jari a tsabar SQUID don gudanar da wani "bincike."

Yace:

"Na yi tunanin, bari in saka $10 (N4000) a wannan don kawai nishadi. Na sami kusan SQUID 661. Yayin da kwanaki suka wuce, sai na fara ganin yana hawa, 1$, 2$, 5$, 10$, 30$, Sai na fara tunanin... Ka yi tunanin idan da zan iya cire kudin nan.

Kara karanta wannan

Mota ta farko da zan hau ni zan kera ta : Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna

"Tabbas, na san cewa ba zan taba cire kudin ba, na gamsu da hakan, amma abin farin ciki ne ganin hakan ya faru."

Dan crypton ya ce bayan kwana biyu farashin SQUID ya tashi zuwa dala 2,000, wanda hakan ke nufin zai samu sama da dala miliyan 1.3.

Sai dai bayan mintuna biyar kacal, sai tsabar ta fado kasa warwas babu komai kuma ya rasa komai nasa.

A cewarsa:

"Yanzu zan iya cewa ni da hamshakin attajiri ne a duniyar crypto a wani lokaci na rayuwata"

Ya kuma kara da cewa yana da masaniya game da zambar crypto kuma ya shawarci sauran 'yan crypto kada su taba "sanya kudi akan tsabar kudi, ko da yaushe ku yi binciken ku kuma ku yi hankali kan abin da kuke zuba jari akai."

Ya ba da shawarar cewa:

"Rashin ikon canza kudin crypto zuwa kudin gaske shine daya daga cikin manyan haduran saka hannun jari a crypto. Za ku iya dawo da kudin ne idan akwai bukatar hakan, don haka kuna iya rasa dukkan 'yan kudaden ku.

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

"Idan darajarsu ta fadi zuwa sifili, ko dai saboda kudin zamba ne ko kuma saboda masu saka hannun jari sun rasa kwarin gwiwa, za a iya barin ku da kudaden crypto mara amfani wadanda ba za ku iya siyarwa ba.

Sabbin tsabobin crypto sun fi hadari fiye da wadanda suka kafu kamar su Bitcoin da Ethereum.

Wani ma an yi wuff da kudadensa

A watan da ya gabata wani dan crypto ya ba da labarin yadda ya yi asarar duk abin da ya mallaka a rayuwarsa yayin da ya sayi tsabar crypto ta SQUID kuma darajarsa ta ragu, inda 'yan damfara suka yi wuff da sama da dala miliyan biyu.

Shi dai dan crypton wanda ya sayi SQUID 5,000 akan $1 kowanne ya gaya wa CoinMarketCap cewa:

“Na rasa duk abin da nake da shi a wannan. Ba zan sake amincewa da su ba. Ko da ingantattun kudaden crypto ne suna matukar canzawa, wanda ke sa su zama masu hadari sosai ga saka hannun jari."

Kara karanta wannan

Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi

'Yan crypto sun tafka mummunar asara yayin da darajar Bitcoin ta dungura kasa

A makon nan kuwa, 'yan crypto sun tafka babban faduwa a ranar Asabar bayan Bitcoin da wasu tsabobin intanet suka rage darajar sama da dala biliyan daya.

Wannan na faruwa ne yayin da 'yan crypto a duniya suka sayar da tsabobin kudaden intanet don daidaituwa da amintattun hannayen jari yayin da bukukuwan Kirsimeti ke gabatowa.

Bitcoin shine mafi daraja a tsabobin kudaden intanet a daraja ta kasuwa, ya fado da 31.6% daga darajar $69,000 mafi girma a shekarar nan a ranar 10 ga Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel