Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi

Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi

  • Wani hamshakin dan kasuwar kasar India, Ajay Munot, ya yanke shawarar yin amfani da kudin da ya tara domin bikin diyarsa
  • Ajay ya bayyana cewa, zai yi amfani da kudin da ya ke tarawa wurin siya wa diyarsa muhimmiyar kyauta idan za ta yi aure
  • A mai makon gagagrumar kyautar, Ajay ya gina gida casa'in a yankinsa a kan fili mai girman kadada biyu inda ya raba wa talakawa gidajen

Wani mutumin kirki mai suna Ajay Munot ya bai wa diyarsa kyauta wacce ba a taba bayarwa ba a matsayin kyautar aure.

Ya ginawa talakawa gidaje casa'in domin shagalin bikin diyar shi inda ya bayar da su kyauta domin karrama ta.

Kafin wannan ranar, mutumin ya kwashe shekaru yana tara kudin shagalin bikin. Amma da lokaci yayi kuma ya ga jama'ar yankin suna fama da talauci, sai ya fada damuwa kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Yadda wata mahaifiya ta sadaukar da rayuwarta domin ɗanta ya tsira

Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi
Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi. Hoto daga YouTube/ANI
Asali: UGC

Amarya ta amince

Da yawan kudin da ya adana domin bikin diyar shi, mutumin ya yi tunanin cewa zai iya amfani da kudin wurin ginawa jama'a gidaje masu kyau.

A yayin da dan kasuwar siyar da suturan ya sanar da diyar shi kan abinda yayi niyya, budurwar ta amince inda tace tabbas wannan tunani ne mai muhimmanci, ANI News suka ruwaito.

Sun bayar da makullan gidan

Ya iya siyan fili mai girman kadada biyu kuma ya gina gidaje har guda casa'in ga wadanda basu da halin siyan gida.

Bayan bikin diyar shi, ita da mijinta sun mika makullan gidajen ga wadanda rabonsu ya tsaga.

Ajay ya ce ya na fatan mutane za su dinga taimako suna badawa a duk lokacin da suke da hali kamar yadda yayi.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 5 an kore shi daga jami'a, ya koma inda ya samu digiri mai daraja ta 1 da lambobin yabo

Matashi ya ziyarci birnin zinari inda mutane ke wanke fuska da shi, bidiyo da hotunan sun gigita jama'a

A wani labari na daban, yayin da wasu suke ganin zinare a matsayin ma’adani mai kimar gaske da tsada, garin Kanazawa ba su dauke shi a matsayin wani kayan gabas ba.

Wani mai yawon bude idanu, Joe Hattab ya ya gano hakan bayan ya kai ziyara wani gari da ke Japan.

Joe, a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, ya nuna wasu yankuna da ke cikin kasar mai arziki da mutanen ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel