A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami

A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami

  • Wani matashi Kassim Mohammed mai shekaru 30 a duniya da ake zargi da fashi da makami ya ce ya saci motoci 30 a cikin shekaru 3 kacal
  • Kassim ya ce ya na da dillalai masu siyan hajar da ya sata a Birnin Kebbi da jamhuriyar Nijar a duk lokacin da ya kwace motar mutane
  • Wanda ake zargin ya ce ya fi jin dadin satar mota kirar Toyota Corolla saboda an fi saurin siyan ta fiye da wasu motoci idan ya sata

Kassim Mohammed matashi ne mai shekaru talatin a duniya wanda ake zargi da fashi da makami. Ya sanar da cewa ya saci motoci talatin a cikin shekaru uku.

Kamar yadda ya bayyana, ababen hawan yana siyar da su ne wurin wasu dillalai da ke Birnin Kebbi da jamhuriyar Nijar inda yace ya fi son satar Toyota Corolla saboda ta fi saukin siyarwa.

Kara karanta wannan

An kama mai faskare saboda fizgar mazakutar mai gidansa da rashin jituwa ya shiga tsakaninsu

A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami
A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Mohammed yana daga cikin 'yan ta'adda 32 da 'yan sanda suka yi ram da su a Abuja a ranar Talata da ta gabata, Punch ta ruwaito.

A cewarsa, "Sau da yawa na kan kai motocin Njiar amma ina da kwastomomi a Birnin Kebbi. Sau biyu ana kai ni gidan yari kuma wasu daga cikin yarana yanzu haka suna gidan yari. Na fi son satar Toyota Corolla saboda an fi siyan ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mai korafi mai suna Abdul Bature, ya gano makwabtansa daga cikin wadanda ake zargi. Ya zargesu da sace wata 'yar uwar shi tare da yi mata fyade bayan karbar kudin fansa daga mijin ta.

Ya kara da zargin cewa wadanda ake zargin sun sace masa shanu kuma 'yan sanda sun taba kama su har sau biyu, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

Bature ya ce, "Bayan siyar da shanun, sun sace diyata, sun yi mata fyade bayan karbar kudin fansa daga wurin mijin ta. Bayan rundunar STS sun kama su, mun tabbatar da cewa su ne.
"Muna da kusanci sosai. Kusan komai tare muke yi. Sun saci shanunmu ashirin da hudu. Ko da 'yan sanda sun sako su, ba za su daina ba. Ya kamata gwamnati ta yi wani abu a kai."

Kakakin rundunar 'yan sanda, Frank Mba, ya ce wadanda ake zargin sun shiga hannu ne sakamakon kokarin rundunonin 'yan sandan Zamfara, Niger, Kaduna, Kebbi da Sokoto.

Kaduna-Abuja: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan bindiga 32, sun samo motoci 17 da AK47 19

A wani labari na daban, jami’an hukumar ‘yan sandan Najeriya sun kama mutane 32 da ake zargin sun aikata laifuka daban-daban, ciki har da garkuwa da mutane, fashi da makamai, sumogal din makamai, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, harkar miyagun makamai, sata, fyade da sauransu.

Kara karanta wannan

BaAmurkiya mai digiri 4 ta gangaro Afrika, ta yi wuff da dan achaba, tace hadin Ubangiji ne

‘Yan sandan sun samu nasarar amsar miyagun makamai kamar bindiga kirar AK47 guda 19, kananun bindigogi da sauran miyagun makamai. Sannan sun samu nasarar amsar motocin sata guda 17 daga wurinsu bayan bincike mai tsanani akan laifukan, Vanguard ta ruwaito.

Cikinsu akwai mutane 6 da suka shahara wurin sace-sace inda aka gano sun saci motoci 6 daga wurare daban-daban ciki har da Nasarawa, Port-Harcourt, Abuja, Kebbi da jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel