Mota ta farko da zan hau ni zan kera ta : Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna

Mota ta farko da zan hau ni zan kera ta : Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna

  • Wani fasihin yaro dan Najeriya, Oyedele Femi Olamide ya bayyana niyyarsa ta hada motarsa ta farko wacce zai tuka a rayuwarsa
  • Yaron wanda ya kammala makarantar sakandare ya hada kananun motoci wadanda ya yi amfani da karfe wurin yinsu inda ya ce ya na kwaikwayon Elon Musk ne
  • Duk da kasancewar Femi mai karancin shekaru, ya iya wakar gambara kuma kwararre ne a fannin zane iri daban-daban

Najeriya kasa ce wacce Ubangiji ya albarkata da mutane masu fasaha a bangarori daban-daban, wani matashi, Femi Olamide ya na daya daga cikinsu.

Yaron mai dumbin baiwar ya bayyana yadda ya hada motoci da karfen aluminum wanda yake amfani da na’urar rimot don yin motsi ba tare da taimakon wani ba.

Ina son yi wa hamshakin mai kudi, Elon Musk, aiki: Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna
Ina son yi wa hamshakin mai kudi, Elon Musk, aiki: Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna
Asali: Original

Femi wanda ya kammala sakandare kuma ya ke zaune a gida tsawon shekaru 3 ya ce yana son ya zama kamar Elon Musk.

Saboda rashin samun damar shiga jami’a, tsawon shekaru 3 ya yi ta kirkire-kirkire daban-daban da hannayensa.

Ya bayyana niyyarsa ta hada wa kansa mota waccce ita zai fara tukawa a wata hira da Legit TV ta yi da shi.

Ya ce ya fara hada motoci ne da kwalaye kafin ya koma amfani da karafa don kada su lalace idan an zuba musu ruwa.

Ya ce yana fatan kera wa kansa motar da zai dinga hawa. Ya ce ya na son zama kamar Elon Musk, mai kudin duniya kuma ya na fatan yin aiki a karkashinsa.

Baya ga kera motoci, Femi ya na yin wakoki masu dadi kuma ya iya zane kwarai da gaske.

'Yan Najeriya sun yi martani

Nan da nan mutane suka fara tsokaci karkashin bidiyon tattaunawar da aka yi da shi.

Inda wani Paul Obomenfo ya ce:

“Yaro mai fasahar gaske. Ka ci gaba da aiki watarana sai labari.”

Peter Johnson ya ce:

“Mai yaron nan yake yi a Najeriya da har yanzu bai shahara ba?
Abraham Godaon ya ce: “Ya nemi taimakon kamfanonin motoci na kasashen waje don su tallafa masa.”

Oshodi Holuwatofunmi tace:

“Yan Najeriya su na da fasaha. Amma ana saurin mantawa da irinsu.”
Ajikobi Shearer Babajide ya yi tsokaci da: “Lokacin da yake wakar ban san sanda na fara kada kaina da jikina ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel