Gwamna Zulum ya lissafo muhimman ayyuka 20 da ya ke fatan yi wa jiharsa a 2022

Gwamna Zulum ya lissafo muhimman ayyuka 20 da ya ke fatan yi wa jiharsa a 2022

  • Kafin shekarar 2022, gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana muhimman ayyuka 20 da yake shirin kammalawa a sabuwar shekarar
  • Daga ciki akwai gyaran tituna, tantance malamai, gyara tsarin karatun almajirai, gyara wasu birane tare da daukar nauyin 'ya'yan jami'an da suka rasa rayukansu
  • A cikin ayyukan, gwamnan ya ce yana so ya horar da ma’aikatan lafiya 1,000 a asibitin koyarwa na jihar Borno a shekarar 2022

Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya lissafo ayyuka 20 da yake da kudirin aiwatarwa a shekarar 2022.

A wata takarda wacce gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, 3 ga watan Disamba, ta bayyana yadda gwamna Zulum ya lissafo kowanne daga cikin ayyukan da ya gabatar a ranar 30 ga watan Nuwamba a Maiduguri yayin bayyana kasafin shekarar ga majalisar jihar.

Kara karanta wannan

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

Gwamna Zulum ya lissafo muhimman ayyuka 20 da ya ke fatan yi wa jiharsa a 2022
Gwamna Zulum ya lissafo muhimman ayyuka 20 da ya ke fatan yi wa jiharsa a 2022. Hoto daga The Governor of Borno
Asali: Facebook

Ga muhimman abubuwa 20 da gwamnan ya ke da kudirin aiwatarwa:

1. Daukar nauyin yara 500 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka halaka iyayensu.

2. Kammalawa da kuma horar da ma’aikatan lafiya 1,000 na asibitin koyarwa ma jihar Borno.

3. Tabbatar da karancin albashin malaman firamare ya kasance N30,000.

4. Jarabawar tantance malamai 3,000.

5. Kulawa da tantance ma’aikatan lafiya da na makarantu.

6. Gabatar da makarantar horar da ‘yan sa kai karkashin masu bayar da shawarwari akan matsalolin tsaro.

7. Daukar nauyin 'ya'yan jami'an CJTF, mafarauta da ‘yan sa kai da suka rasa rayukansu wurin yakar ‘yan ta’adda.

8. Tallafa wa matan da suka rasa mazajensu.

9. Farfado da makarantun da aka rufe saboda rashin tsaro da tabbatar da tsaron yankuna, za a fara da Dikwa, Monguno da kuma kafa makarantu bibbiyu a kowacce mazaba.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

10. Gyara ginin kwalejojin ilimi .

11. Samar da cibiyar koyawa mata sana’o’in dogaro da kai.

12. Gina kwalejoji na ilimin addinin musulunci a Gamboru-Ngala, Malam Fatori, Damboa da Kwayakusar.

13. Dawo da mutane cikin Malam-Fatori da Gudumbali.

14. Tabbatar da ayyukan gyara tare da mayar da 'yan gudun hijira a Malam-Fatori da Kala-Balge.

15. Gyara a ilimin Almajirai.

16. Gabatar da Keke Napep 500 a jihar da dawo da harkokin shi a jihar.

17. Ganin bayan bangar siyasa ta hanyar daukar nauyin yara 150 a ECOMOG wadanda suka sa hannun daina bangar siyasa.

18. Tallafa wa matasa 1,000 daga Biu, 1,000 daga Monguno da Bama ta hanyar sana’o’in dogaro da kai.

19. Gyara titin Maiduguri zuwa Damboa

20. Cigaba da fadada birane.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel