Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

  • Gwamnatin Gwamna Ganduje ta musanta labarin da ke yawo na cewa ta garkame ofishin lauyan Shekarau bayan hukuncin kotu
  • Kamar yadda hukumar kula da filauye ta jihar tace, ta garkame ginin ne mallakin Isiyaka Rabi’u & Sons kan rashin biyan haraji
  • A cewar hukumar, a ranar Laraba kadai, ta rufe gine-gine kusan talatin bayan da ta aike musu ta notis na jan kunne tun a watan Satumba

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi karin haske kan dalilin da yasa ta garkame ginin ofishin Barista Nuraini Jimoh.

Daily Trust ta ruwaito yadda Jimoh, daya daga cikin lauyoyin Malam Ibrahim Shekarau da wasu ma'aikatansa aka garkamesu na tsayin sa'o'i a cikin ofishinsa bayan umarnin gwamnatin

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau
Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Lamarin ya auku ne bayan sa'o'i 24 da tsagin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na Shekarau ya lallasa Gwamna Abdullahi Ganduje a kotu.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin Kotu, Gwamnatin Ganduje ta kwace ofishin Lauyan tsohon Sarki Sanusi a Kano

Wata babbar kotu da ke Abuja ta jadadda cewa, zaben shugabannin da bangaren jam'iyyar na Shekarau suka yi shi ne daidai kuma suka rushe shugabannin jam'iyyar na tsagin Ganduje.

Da yawa sun alakanta matakin da gwamnatin ta dauka kan radadin da tsagin Ganduje suka ji sakamakon hukuncin kotun, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda da hukumar kula da gidaje ta fitar, ta ce gwamnatin ba ta lauyan ta ke ba sai dai ta mamallakin ginin.

Murtala Shehu Umar, mai magana da yawun hukumar, ya kwatanta rahoton da zancen kawai inda ya kara da cewa an rufe gine-gine masu yawa a ranar.

"Gwamnatin jihar ta rufe gini mallakin Isiyaka Rabi’u & Sons a C14/C16 kan titin Murtala Muhammad ta karkashin kwamitin hukumar kula da filaye."

Kara karanta wannan

'Yan banga sun jawo 'yan bindiga sun hallaka mazauna a Sokoto, gwamnati ta fusata

"Kwamitin ya mika takarda ga mai ginin a ranar 14 ga watan Satumba kuma an bashi wata daya da ya zo ya biya kudin harajin da ake bin shi tun daga shekarar 2016 zuwa 2021.
“Mun rufe a kalla gine-gine talatin a ranar 1 ga watan Disamba a sassan jihar. Wuraren sun hada da Zoo road, Zaria road da Ibrahim Taiwo road.
“Hakazalika, an garkame wasu gini 7 da ke kan titin Murtala Muhammad bayan an mika takardar jan kunne tun wata daya da ya gabata amma ba su yi martani ba. Don haka kwamitin zai cigaba da rufe duk wata kadar da mamallakin ta ya ki bin doka.
“A matsayinmu na jami'an hukumar, takardu sun nuna cewa ginin mallakin Isiyaka Rabi’u & Sons ba Barista Nuraini Jimo ba. Damuwar mu ita ce mai ginin ba wai wanda ke haya ba," takardar tace.

Gwamnatin Kano tare da yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau a ofishinsa

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu na rushe zaɓen ɓangarensa

A wani labari na daban, Jami'an ma'aikatar filaye tare da yan sanda sun rufe ofishin Lauya Nureini Jimoh, SAN, da ke 16c Murtala Mohammed Way a Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Jimoh, a ranar Talata shine ya wakilci bangaren Sanata Ibrahim Shekarau inda suka yi nasara kan bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a rikicin shugabancin jam'iyyar APC a Kano.

Lauyan ya tabbatar wa Daily Nigerian da cewa an rufe ofishinsa yayin da shi da sauran ma'aikatansa suke ciki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel