Cikaken Jerin Sunayen Malamai 233 Da Gwamnatin Kaduna Ta Kora Kan Satifiket Ɗin Bogi

Cikaken Jerin Sunayen Malamai 233 Da Gwamnatin Kaduna Ta Kora Kan Satifiket Ɗin Bogi

  • Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da cikakken sunayen malaman makaranta da ta kora saboda satifiket din bogi
  • Mr Tijjani Abdullahi, Shugaban Hukumar Ilimin ya ce baya ga korar malaman za a tura suayensu zuwa Ma'aikatr Sharia don maka su a kotu
  • Makarantun da daliban fito sun hada da Cibiyar Horas da Malamai, NTI, Kwallejin Ilimi ta Zaria, FCE, Kwallejin Nuhu Bamalli, Zaria da wasu

Kaduna - A ranar Alhamis, Mr Tijjani Abdullahi, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya, ya sanar da cewa za a sallami malamai 233 daga ciki kan zargin gabatar da sakamakon kammala karatu na bogi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Abdullahi ya ce baya ga korarsu daga aiki, za a kuma maka su a kotu.

Cikaken Jerin Sunayen Malamai 233 Da Gwamnatin Kaduna Ta Kora Kan Satifiket Din Bogi
An saki sunayen malamai 233 da gwamnatin jihar Kaduna ta kora daga aiki. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Satifiket din makarantun da suka gabatar

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin El-Rufa'i za ta sallami Malamai 233 kan laifin amfani da takardun boge

Ya ce malaman sun gabatar da satifiket din makarantun da suka hada da Cibiyar Horas da Malamai, NTI, Kwallejin Ilimi ta Zaria, FCE, Kwallejin Nuhu Bamalli, Zaria, Kwallejin Ameer Shehu Idris da Kwallejin Ilimi ta Gidan Waya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sakamakon bogin da malaman suka gabatar, sun yi ikirarin sun samu shaidan karatu ta NCE, Diploma a Larabci, Diploma a Koyar da Ilimin Addinin Musulunci da Jagoranci a aikin gwamnati.

Ya ce kawo yanzu hukumar ta tabbatar da satifiket guda 451 ta hanyar tuntubar makarantu 13, amma 9 cikinsu ba su basu amsa ba tukunna, rahoton Daily Trust.

Za a gurfanar da su a kotu bayan korarsu

Shugaban ya ce:

"Amsoshin da muka samu ya nuna malamai 233 sun gabatar da satifiket din bogi. Hakan ya nuna kashi 51 cikin satifiket 451 bisa la'akari da amsoshin da aka basu daga makarantun. Makaranta guda daya ta yi watsi da satifiket 212 cikin 233.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

"Hukumar za ta sallami malaman 233 da suka gabatar da satifiket din bogi daga ciki, sannan za ta tura bayannansu zuwa Ma'aikatar Shari'a domin a fara shirin shari'a da su kan gabatar da takardun na bogi."

Latsa nan domin ganin cikakken jerin sunayen malaman da aka kora.

Asali: Legit.ng

Online view pixel