Da dumi-dumi: Gwamnatin El-Rufa'i za ta sallami Malamai 233 kan laifin amfani da takardun boge

Da dumi-dumi: Gwamnatin El-Rufa'i za ta sallami Malamai 233 kan laifin amfani da takardun boge

  • Gwamnatin jihar Kaduna zata fitittiki Malaman Makaranta sama da dari biyu kan laifin amfani da takardun bogi
  • Hukumar SUBEB ta jihar me alhakin kula da kananan makarantu ta gudanar da bincike kansu
  • A cewar shugaban hukumar, an tura sunayen wadannan Malamai jami'o'in da suka yi ikirarin sun yi karatu

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufa'i ta sanar da cewa za ta sallami Malaman makaranta 233 bisa gabatar da takardun boge.

Shugaban hukumar ilmin kananan makarantun jihar SUBEB, Tijjani Abdullahi, ya sanar da hakan ranar Alhamis, 2 ga Disamba, a hira da manema labarai.

Gwamnan Kaduna da kansa ya daura wannan jawabi a shafinsa na Facebook.

Tijjani yace:

"Kawo yanzu, an tantance takardu 450 ta hanyar tuntubar makarantun da suka bada. Makarantu 9 cikin 13 sun bamu amsa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dattijai ya rigamu gidan gaskiya

"Amsoshin da muka samu sun nuna cewa Malamai 233 sun gabatar da takardun boge. Jami'a daya ciki tace takardu 212 na bogi ne."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hukumar za ta sallami Malaman 233 yayinda aka tura sunayensun ma'aikatar Shari'a domin gurfanar da su kan laifin zamba."
Da dumi-dumi: Gwamnatin El-Rufa'i
Da dumi-dumi: Gwamnatin El-Rufa'i za ta sallami Malamai 263 kan laifin amfani da takardun boge Hoto: Governor of Kaduna
Asali: Facebook

Shugaban hukumar ya kara da cewa a yau Alhamis za'a daura sunayen wadannan Malamai 233 a shafi yanar gizo don kowa ya gani.

El-Rufai ya sauya tsarin aikin gwamnatin Kaduna, za a koma aikin kwana 4 a mako

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sabon tsarin kwanakin aikin gwamnati a fadin jihar Kaduna.

Kamar yadda gwamnan ya sanar a shafinsa na Facebook, za a fara wannan sabon salon ne zuwa ranar 1 ga watan Disamban wannan shekarar.

A cewar gwamnan:

"Gwamnatin jihar Kaduna za ta fara sabon sauyin aikin kwanaki hudu a mako a jihar. Na wucin-gadi, za a bar ma'aikatan gwamnati su dinga aikin kwana daya daga gida.

Kara karanta wannan

Labari cikin Hotuna: Yadda Yan daba suka kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau a Kano

"An tsara wannan ne domin taimakawa wurin habaka yawan aiki, kawo inganci tsakanin rayuwar ma'aikaci da aikinsa tare da bai wa ma'aikata damar samun lokaci da iyali, hutawa da kuma noma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel