Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

  • An samu rahotanni cewa yan ta'addan ISWAP sun sake kai hari a jihar Borno, sun sace wasu ma'aikatan gwamnatin jihar
  • Jami'an gwamnatin suna duba wasu ayyukan ginin titi ne a karamar hukumar Chibok a lokacin da lamarin ya faru
  • Wani babban jami'in gwamnati ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa abin ya faru ne a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Disamba

Jihar Borno - Miyagun ƴan ta'addan kungiyar Islamic State in West Africa, ISWAP, sun sace ma'aikatan gwamnatin jihar Borno a ƙalla biyar, rahoton Daily Trust.

An sace ma'aikatan ne a ranar Laraba, a lokacin da suka saka ido a kan aikin ginin titin Chibok-Damboa.

Lamarin ya faru ne kusa da Wovi, a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Chibok.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno
An rahoto cewa yan kungiyar ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan jihar gwamnatin Borno su biyar. Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa ɗaya daga cikin ma'aikatan, direba, ya tsira daga harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani babban jami'i ya tabbatar wa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin yana cewa:

"Eh, da gaske ne, abin bakin ciki ne kuma abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan yana damun mu.
"Sace su da aka yi ya firgita mu. Zan iya tabbatar maka cewa an sace su a safiyar yau."

Bayan shafe fiye da wata 6 cikin duhu, Zulum ya sanar da ranar da za a dawo da lantarki a Maiduguri

A baya, kun ji cewa Gwamna Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno ya bada tabbacin cewa za a dawo da wutar lantarki a Maiduguri da kewaye cikin kwanaki 30, Daily Trust ta ruwaito.

Babban birnin jihar ta Borno ta kasance cikin duhu tun lokacin da 'yan ta'adda suka lalata layukan lantarkin garin da ke hanyar Maidugri zuwa Damaturu watanni 11 da suka gabata.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Gwamnatin Kano tare da 'yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau da wasu mutane a cikin ofishinsa

Yayin da ya ke gabatar da kasafin kudi ta shekarar 2022 a gaban majalisar jihar, a ranar Talata, gwamnan ya ce ana kokarin dawo da lantarki a garin kamar yadda ya zo a ruwayar ta Daily Trust.

'Yan sanda sun hana 'yan ta'addan Boko Haram sace soja da fasinjoji 15 a Borno

A wani labarin, jami'an yan sanda sun hana wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sace wani jami'in soja a jihar Borno, majiyoyi suka shaidawa The Cable.

Sojan, wanda ke aiki a bataliyar sojoji da ke Marte, yana kan hanyarsa daga Damaturu zuwa Maiduguri ne lokacin da yan ta'addan suka kai hari.

Majiyoyi sun ce yan sandan sun kuma hana yan ta'addan sace wasu fasinjoji guda 15, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel