El-Rufai ya sauya tsarin aikin gwamnatin Kaduna, za a koma aikin kwana 4 a mako

El-Rufai ya sauya tsarin aikin gwamnatin Kaduna, za a koma aikin kwana 4 a mako

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sabon tsarin aikin gwamnati a jihar inda za a dinga aikin kwanaki hudu a mako
  • Kamar yadda El-Rufai ya sanar, wannan tsarin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Disamba kuma an yi shi ne domin cimma wasu manyan manufofi
  • A cewar gwamnan, baya da malaman makaranta da ma'aikatan asibiti, ranar Juma'a ma'aikata za su kasance a gida inda za su yi aikinsu ta yanar gizo

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sabon tsarin kwanakin aikin gwamnati a fadin jihar Kaduna.

Kamar yadda gwamnan ya sanar a shafinsa na Facebook, za a fara wannan sabon salon ne zuwa ranar 1 ga watan Disamban wannan shekarar.

Da duminsa: Ma'aikatan Kaduna za su koma aikin kwanaki 4 a mako
Da duminsa: Ma'aikatan Kaduna za su koma aikin kwanaki 4 a mako. Hoto daga Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

A cewar gwamnan:

"Gwamnatin jihar Kaduna za ta fara sabon sauyin aikin kwanaki hudu a mako a jihar. Na wucin-gadi, za a bar ma'aikatan gwamnati su dinga aikin kwana daya daga gida.

Kara karanta wannan

Wani nau’in cutar COVID-19 mai mugun hadari da bai jin magani ya bulla a kasashen Afrika

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An tsara wannan ne domin taimakawa wurin habaka yawan aiki, kawo inganci tsakanin rayuwar ma'aikaci da aikinsa tare da bai wa ma'aikata damar samun lokaci da iyali, hutawa da kuma noma.
"An dauka wannan matakin ne sakamakon darasin da aka koya daga annobar korona wanda ke bukatar sakin tsoffin tsarikan aiki tare da rungumar aiki ta yanar gizo kuma daga gida."

Kamar yadda takardar da ta fito daga gidan gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana, za a fara wannan tsarin ne daga ranar daya ga watan Disamban wannan shekarar.

Daga wannan ranar, an sauya sa'o'in aikin ma'aikatan gwamnati inda zai koma daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyar na yammaci, Litinin zuwa Juma'a.

Dukkan ma'aikatan gwamnati baya da malaman makaranta da masu aikin asibiti, za su dinga aiki daga gida a ranakun Juma'a. Wannan tsarin aikin zai cigaba har zuwa lokacin da gwamnati ta shirya zuwa matakin gaba na sauyin a jihar.

Kara karanta wannan

Shaidar EFCC: Da kaina na ciro wa Jang biloyoyin naira babu takarda

Idan ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 ba za su iya biyan albashi ba a 2022, El-Rufai

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce matsawar ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba a 2022, Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a Abuja a wani taro na World Bank Nigeria Development Update, na watan Nuwamba 2021, inda yace don gudun faruwar hakan, a shirye gwamnoni suke don amincewa da cire tallafin man fetur din.

A cewarsa, in har ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba a 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel