Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dattijai ya rigamu gidan gaskiya

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dattijai ya rigamu gidan gaskiya

  • Tsohon shugaban majalisar dattijai, Dakta Joseph Wayas, ya rigamu gidan gaskiya a birnin Landan
  • Rahotanni sun bayyana cewa Dakta Wayas ya mutu ne bayan fama da rashin lafiya, a cewar gwamnan Cross Ribas, Ben Ayade
  • Ayade ya yi ta'aziyya ga iyalan mamacin, kuma ya tabbatar musu ba su kaɗai suka yi rashi ba, Najeriya baki ɗaya ta shiga jimami

Cross River - Tsohon shugaban majalisar dattijai a jamhuriya ta biyu, Dakta Joseph Wayas, ya rigamu gidan gaskiya.

The Nation ta rahoto cewa Dakta Wayas, wanda ya jima yana kwance bashi da lafiya, yana samun kulawa, ya mutu ne a wani asibiti a Birnin Landan.

Gwamnan jihar Cross Ribas, Farfesa Ben Ayade, shine ya tabbatar da mutuwar Dakta Wayas a wata sanarwa da gwamnatinsa ta fitar.

Dakta Wayas
Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dattijai ya rigamu gidan gaskiya Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Gwamnan ya koka da wannan rashi, inda ya bayyana mutuwar Wayas da wani babban rashi ga jihar Cross Ribas da ma Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin El-Rufa'i za ta sallami Malamai 233 kan laifin amfani da takardun boge

A sanarwan, wacce hadimin gwamnan ta ɓangaren Midiya da yaɗa labarai, Christian Ita, ya fitar, Ayade yace tafiyar Wayas ta bar wani gibi da zai wahalar cikewa.

Waye Dakta Wayas?

The Cable ta rahoto Farfesa Ayade yace:

"Jihar Cross Ribas baki ɗaya ta shiga cikin radaɗi da jimami bisa rasuwar ɗaya daga cikin ƴaƴanta da take ji da su. Da wahala samun irin su, Mutuwar Dakta Wayas babban rashi ne ga jiharmu da Najeriya baki ɗaya."
"A lokacin da ya jagoranci majalisar dattijan Najeriya, Dakta Wayas, ya bada ɗumbin gudunmuwa wajen kara gina demokaradiyya a Najeriya ta hanyar amfani da kujerarsa ta babbar majalisa."
"Haka nan kuma tun bayan da ya yi ritaya daga siyasa, tsohon shugaban majalisar dattawan bai yi ƙasa a guiwa ba wajen cigaba da taka rawar gani a matsayin uba da kuma daidaita al'amuran siyasa a jihar mu."

Kara karanta wannan

Labari cikin Hotuna: Yadda Yan daba suka kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau a Kano

Gwamnan ya jajantawa iyalan marigayin

Daga nan gwamnan ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayi Dakta Wayas, kuma ya tabbatar musu da cewa ba su kaɗai suke jin raɗaɗin rasuwarsa ba, kowa na jin kwatankwacin abinda suke ji.

A wani labarin na daban kuma mutane sun shiga tashin Hankali yayin da aka tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa an tsinci gawar wasu mutum biyu, mace da namiji a cikin mota.

Hukumar yan sanda tace namijin yana da mata har da ƴaƴa, yayin da ita kuma macen za'a ɗaura mata aure a watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel