Yadda 'yan fashi su ka yashe maƙuden kuɗi daga ATM ɗin wani banki a cikin dare

Yadda 'yan fashi su ka yashe maƙuden kuɗi daga ATM ɗin wani banki a cikin dare

  • ‘Yan fashi sanye da sutturun ‘yan sanda sun afka wa wani banki da ke Ikirun, hedkwatar Ifelodun a cikin jihar Osun
  • Sai dai an samu bayanai akan yadda su ka kasa shiga cikin bankin inda su ka afka wa ATM din bankin su ka yashe kudaden da ke ciki
  • Sai da su ka daddaure wani mafarauci da ke gadin bankin yayin da sauran suka tsere neman agaji, daga nan su ka yi satar su ka tsere

Jihar Osun - ‘Yan fashi sanye da sutturu irin na ‘yan sanda sun afka wani banki da ke Ikirun, Hedkwatar Ifelodun da ke cikin jihar ta Osun.

The Nation ta gano yadda su ka kasa shiga cikin bankin, su ka afka wa ATM din bankin inda su ka cire duk kudaden da ke ciki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace basarake da matarsa da mutane da dama a Katsina

Yadda ‘yan fashi su ka yashe kudi daga ATM din wani banki a jihar Osun
Yan fashi sun sace kudade masu dimbin yawa daga ATM din banki a Osun. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Sun isa wurin da misalin karfe 2 na dare

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya daga mazauna yankin ta bayyana yadda ‘yan fashin su ka afka bankin da misalin karfe 2 na dare.

Majiya daga jami’an tsaro ta sanar da wakilin The Nation yadda ‘yan fashin su ka isa wurin da yawansu.

Kamar yadda majiyar ta shaida:

“Yan fashi da yawansu sun afka bankin sanye da sutturun ‘yan sanda. Sun daure wani mafarauci da ke gadin bankin yayin da sauran su ka tsere su na neman dauki.
“Kafin ‘yan sanda su isa wurin, har sun balle ATM din bankin sun yashe kudaden da ke ciki. Amma ba su samu damar shiga bankin ba.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Yemisi Opalola ya tabbatar da aukuwar harin.

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

Kara karanta wannan

Shugaban Koriya ta Arewa ya haramtawa 'yan ƙasarsa saka irin tufafinsa, ya hana shaguna sayar da irin tufafin

A wani labarin, hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta nemi taimakon 'yan Nigeria wurin neman wasu mutane hudu da ta ayyana nemansu ruwa a jallo kan damfara.

Hukumar a shafinta na Facebook, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba ta ayyana neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo.

EFCC ta ce ana bincikar wadanda ake zargin ne kan laifuka masu alaka da damfara. Hukumar ta bukaci duk wani da ke da bayani mai amfani dangane da inda mutanen suke ya tuntubi ofisoshinta a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel