Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana tsoronta ga yadda adadin 'yan Najeriya ke karuwa zuwa wani adadi mai yawa
  • Gwamnati ta ce, wannan babban lamari ne da ke bukatar magancewa cikin gaggawa don tsiratar da kasar
  • Hakazalika, gwamnati ta hango yadda Najeriya za ta zama kasa ta uku a yawa a duniya idan ba a kula ba

Abuja - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce kiyasin yawan al’ummar Najeriya na da ban tsoro, don haka akwai bukatar a samar da matakan da za a bi don dakile karuwar al’ummar kasar.

Mista Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja yayin kaddamar da wani littafi.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha
Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole a yi wani abu, inji gwamnatin Buhari | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Littafin, wanda Dokta Manassah Jatau, mataimakin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya mai ritaya, an saka masa suna, “A Sociology for Medical Practice.”

Kara karanta wannan

Karyar takunkumi Gwamnati ke yi, Sanatoci sun gano ana daukar yaran manya aiki a boye

Jaridar The Guardian ta ruwaito Mustapha na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan aka yi la’akari da shekaru goma ko ashirin, Najeriya za ta zama kasa ta uku a yawan al’umma, bayan China da Indiya.
“Akwai bukatar gaggawa a gare mu mu fara tsara wannan karuwar.
“A yanzu haka, muna fama da yawan matasa kuma ba mu iya samar da wata mafita ga wasu korafe-korafe a kasar nan."

SGF ya yaba wa marubucin saboda zurfin fahimtarsa game da batutuwan jagoranci wajen tantance tasiri da ingancin kungiyoyi, musamman a zahiri da na tattalin arziki, kamar yadda ya rubuta a cikin littafin.

Ya kamata a bunkasa harkar magungunan gargajiya

Mustapha ya kuma kara jaddada bukatar bunkasa harkar magungunan gargajiya a Najeriya, inda ya kara da cewa, harkar za ta samar da ayyukan yi, da bunkasa kayayyakin harhada magunguna na kasar, tare da inganta tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

A cewarsa:

“Har ila yau, akwai bukatar bullo da magungunan gargajiya. Hakan zai rage matsayin da ‘yan Najeriya ke ziyartar wasu kasashe domin jinya."

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Mista Adewale Adeniyi, Mataimakin Kwanturolan-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), ya yabawa Jatau kan aikin da ya yi.

Adeniyi ya lura cewa shugaban na Kwastam mai ritaya ya bar tarihi a hidimar NCS, wanda ya cancanci a yi koyi da shi, ya kara da cewa marubucin ya yi nasarar auren ilimin zamantakewa da likitanci a lokaci guda.

Farfesa Ibrahim Njodi, tsohon shugaban jami’ar Maiduguri, wanda ya yi nazarin littafin, ya ce littafin ya kunshi ilimin likitanci da ilimin zamantakewa.

A cikin jawabin nasa, Jatau ya bayyana cewa:

"Mutum mai zaman kansa ne kuma al'amuran zamantakewa da yawa suna shafar lafiyarsa, sannan abubuwan da ke haifar da yawancin cututtuka suna da alaka da zamantakewa."

Ya bayyana cewa littafin zai taimaka wajen gane magani, da kuma hana afkuwar cututtuka kamar yadda ya jaddada yanayin rayuwa a cikin al’umma da kuma kawar da illa ga lafiya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Jirgin kamfanin Air Nigeria zai fara tashi a shekara mai zuwa

Don haka Jatau ya yi kira ga gwamnati, malamai, likitoci da sauran jama’a da su yi nazari sosai kan littafin, su yi amfani da shi wajen tattaunawa da bincike.

Wahalhalu 5 da 'yan Najeriya za su shiga idan man fetur ya koma N340, Shehu Sani

A wani labarin, sanata Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna, ya yi magana kan abubuwan da ‘yan Najeriya za su fuskanta idan farashin man fetur ya koma Naira 340 kan kowace lita.

Kalaman Sani sun biyo bayan sanarwar da Babban Manajin Darakta kuma Babban Jami’in NNPC ya yi cewa farashin man fetur na iya cillawa zuwa N320 ko N340 kan kowace lita bayan cire tallafin a shekarar 2022.

Da yake magana a shafinsa na Facebook, tsohon Sanatan ya bayyana abin da zai faru na kunci idan aka fara sayar da fetur a farashi mai tsada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel