Kaso 85 cikin 100 na yan Najeriya ba su da rikon amana, dama kawai suke so, Sheikh Giro Argungu

Kaso 85 cikin 100 na yan Najeriya ba su da rikon amana, dama kawai suke so, Sheikh Giro Argungu

  • Babban malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Abubakar Giro, yace mafi yawan yan Najeriya ba su da rikon Amana
  • Shehin malamin ya bukaci baki ɗaya yan Najeriya su koma ga Allah matukar suna son zaman lafiya mai dorewa ya dawo
  • Yace rokon Allah ba tare da gajiya ba ne kaɗai mafita daga wannan ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fama da shi

Nasarawa - Shahararren malamin addinin islama, Sheikh Abubakar Giro Argungu, ya bayyana cewa kashi 85 cikin ɗari na yan Najeriya ba su da gaskiya wajen rike amana.

Aminiya Hausa tace Sheikh Giro, ya yi wannan furucin ne a wurin wani taron wa'azi da aka shirya don murnar aure a jihar Nasarawa.

Babban malamin ya yi kira ga yan Najeriya baki ɗaya su guji aikata cin hanci da rashawa, kuma su rinka kwatanta adalci da tsare gaskiya a rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na takarar shugaban kasa a 2023

Sheikh Abubakar Giro
Kaso 85 cikin 100 na yan Najeriya ba su da rikon amana, dama kawai suke so, Sheikh Giro Argungu Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Addu'a ce kaɗai mafita a yanzu - Sheikh Argungu

Shehin malamin ya bukaci mutanen Najeriya kada su gajiya, su cigaba da addu'a Allah ya kawo karshen ƙalubalen tsaro da yaƙi ci yaƙi cinye wa a ƙasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa a halin da kasar nan ke ciki yanzun, Addu'a ce kaɗai mafita ɗaya tilo da zata dawo da zaman lafiya da kuma dunƙulewa a Najeriya.

Malamin yace:

"Matuƙar muka dage da rokon Allah (SWA), to zai amsa mana ya kawo karshen ta'addancin yan bindiga, kuma ya kawo zaman lafiya da aminci, da kuma cigaban ƙasa."

Malam Abubakar Giro, ya yi wannan kira ne a wurin taron wa'azin aure da ya gudana a Umaisha, karamar hukumar Toto, jihar Nasarawa.

Legit.ng Hausa ta gano cewa an shirya wannan wa'azi ne domin murnar auren mata ta uku da kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi ya yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta shiga damuwa kan yadda ake mutuwa daga cutar Maleriya

A wani labarin na daban kuma Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023

Sheikh Sani Yahaya Jingir yace babu wanda ya isa ya siyar da kuri'un mutane da sunan karba-karba a 2023.

Shehin Malamin ya kira tsarin da wani abu mai kama da caca, kuma a cewarsa mutane kada su yarda da shi kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel