Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023

  • Sheikh Sani Yahaya Jingir yace babu wanda ya isa ya siyar da kuri'un mutane da sunan karba-karba a 2023
  • Shehin Malamin ya kira tsarin da wani abu mai kama da caca, kuma a cewarsa mutane kada su yarda da shi kwata-kwata
  • Jingir ya yi kira ga yan Najeriya su tabbata sun zaba sun darje a babban zaben 2023 domin kada a sake samun matsala

Jos, Plateau -Shugaban majaisar malamai na ƙungiyar Izala reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, yace ba zasu sake yarda yan siyasa su yaudare su ba

Aminiya Hausa ta rahoto malamin na cewa babu wani ɗan siyasa da zai je ya siyar da kuri'unsu da sunan mulkin karɓa-karba a zaɓen 2023.

Shikh Jingir ya yi wannan furuci ne yayin da yake wa'azi a wurin wa'azin ƙasa da ƙungiyar ta saba shiryawa, wanda ya gudana a Jingir.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani mutum ya hargitsa zaman lafiyar banki kan batun BVN

Sheikh Jingir
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023 Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A jawabinsa, Jingir yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kada mu sake mu yarda wani ɗan siyasa ya je ya siyar da kuri'un mu da sunan yarjejeniyar tsarin mulkin karba-karba a babban zaɓen 2023."
"Wannan tsarin da yan siyasa ke magana a kansa tamkar wata caca ce, kuma yana nufin wasu tsirarun mutane yan siyasa sun maida yan ƙasa tamkar kayan su."

Mu mallakin Allah ne - Jingir

Jingir ya kara da cewa mutane ba bayin yan siyasa bane da zasu juya su yadda suka ga dama, mutane bayin ubangiji Allah ne.

"Kuri'un mu na hannun mu kuma mu zamu zaɓi wanda muke so idan muka ga ya dace kuma yana da manufofi masu kyau."
"Don haka kada mu sake wasu su maida kuri'un mu marasa amfani, har wani ya samu ikon zuwa bada yawun mu ba, ya bada kuri'un mu."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda sojoji suka ladabtar da wani mutum da ya karya dokar hanya a Abuja

Wane mutane ya kamata mu zaɓa a 2023?

Sheikh Yahaya Jingir ya yi kira ga yan Najeriya baki ɗaya su fita kwansu da kwarkwata su zabi mutanen kirki a babban zaɓen 2023 dake tafe.

A cewarsa akwai bukatar yan Najeriya su kula wajen tantance wanda zasu zaɓa, kada su zaɓi waɗan da zasu mance da al'ummar su.

A wani labarin na daban kuma Wani Dalibin jami'a ya lakadawa lakcara mace dukan kawo wuka daga neman taimako

Wani ɗalibin dake 400- Level a jami'ar Ilorin (UNILORIN) ya lakaɗawa malamarsa a jami'a dukan kawo wuka.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, lokacin da ɗalibin ya je ofishin malamar neman ta taimaka masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel