Ku rufe dukkan coci ko kuma mu kawo muku hari: Ƴan bindiga sun rubuta wa kiristocin Zamfara wasika

Ku rufe dukkan coci ko kuma mu kawo muku hari: Ƴan bindiga sun rubuta wa kiristocin Zamfara wasika

  • Wasu yan bindiga sun aika wa kiristoci mazauna jihar Zamfara wasika suna musu barazanar cewa su rufe cocinsu
  • Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Zamfara ta tabbatar da batun wasikar tana mai cewa ta dauki matakan dakile harin
  • Kiristocin na jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan barazanar sannan sun roki al'umma su taimaka musu da addu'a

Wasu kungiyoyin yan bindiga sun rubuta wa kiristocin jihar Zamfara, Arewa maso yammacin Nigeria waska sun umurci su rufe coci-cocinsu idan ba haka ba su kai musu hari, SaharaReporters ta ruwaito.

Rundunar yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar wa SaharaReporters da wannan barazanar inda suka ce, 'Muna bincike kan barazanar.'

Ku rufe dukkan coci ko kuma mu kawo muku hari: Ƴan bindiga sun rubuta wa kiristocin Zamfara wasika
Yan bindiga sun aika wa kiristocin Zamfara wasikar barazana. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Mohammed Shehu, ya shaida wa wakilin majiyar Legit.ng cewa sun san da wasikar barazanar.

Ya ce:

"Eh, zan iya tabbatar maka cewa gaskiya ne, an aike wa kiristocin jihar Zamfara wasika cewa su dena ibadojinsu su rufe coci-cocinsu.
"Hasali ma, yan sandan ne suka sanar da kiristocin jihar Zamfara game da barazanar.
"Kazalika, kwamishinan 'yan sanda, CP, ya gayyaci shugabannin kungiyar kiristocin Nigeria, CAN, a jihar domin tattauna matakan tsaro a coci-cocin."

Ya cigaba da cewa:

"Don haka, an tura jami'an yan sanda na musamman kuma CP din ya tura jami'ai na musamman don su rika sintiri tare da bawa masu bautan tsaro musamman ranar Lahadi.
"Kazalika, mun tura jami'an yan sanda masu farin kaya domin su rika tattara bayanan sirri domin gano dalilin da yasa aka aika wasikar."

Shugabannin kirista sun magantu kan lamarin

A ranar Lahadi, shugaban kirista, wanda ya yi magana amma ya bukaci a sakaya sunansa ya roki a taya su da addu'a game da halin da suke ciki a Zamfara da sauran sassan arewacin Nigeria.

Wani sashi cikin jawabinsa:

"Mu yi wa kiristocin arewacin Nigeria addu'a, musamman jihar Zamfara domin a bamu wa'adin watanni uku mu rufe dukkan cocin mu a jihar.
"An lissafa wasu coci da za a kai wa hari daga nan zuwa Disamba, duk da cewa cocin da za a kai wa harin suna wajen gari ne a cewar kungiyar fulanin, muna ganin dabara ce.
"An tura wa yan sanda, DSS, da NSCDC da sauran hukumomin tsaro wasikar kuma sun ce sun samu sakon."
"An umurci kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, ta fadawa dukkan coci su rika rufe cocinsu karfe 5 na yamma daga wannan zuwa wata uku."

Sakamakon barazanar, wasu kiristoci na tunanin yin hijira daga Zamfara.

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

A wani rahoton kun ji cewa Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.

Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel