Kasurgumin mai garkuwa da mutane ya mutu a gidan yari yayin jiran hukunci

Kasurgumin mai garkuwa da mutane ya mutu a gidan yari yayin jiran hukunci

  • Wani kasurgumin mai garkuwa da mutane ya mutu a gidan yari yayin da yake ci gaba da jiran shari'a
  • An rahoto cewa, Chiemeka Arinze ya mutu ne sakamakon wata gajeriyar rashin lafiya da ya yi a gidan yari
  • Ana tuhumar Arinze da sauran 'yan tawagarsu da laifukan kitsa sace wani attajiri a gaban wata kotu da ke Ikeha

Legas - Chiemeka Arinze, wanda ake tuhuma da laifin sace mutane tare da hamshakin attajirin nan mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya mutu a gidan yari, Vanguard ta ruwaito.

Evans yana fuskantar shari’a tare da Joseph Emeka, Chiemeka Arinze da Udeme Upong, kan yunkurin yin garkuwa da Cif Vincent Obianodo, shugaban kamfanin Young Shall Grow Motors, a gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na wata kotun manyan laifuka ta Ikeja.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa motar kwamishina wuta a Kogi

Ya mutu yayin jiran shari'a
Da dumi-dumi: Kasurgumin mai garkuwa da mutane ya mutu a magarkama yayin jiran hukunci | Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

Suna fuskantar tuhume-tuhume bakwai da suka hada da kisan kai, yunkurin kisa, hada baki don yin garkuwa da mutane, yunkurin garkuwa da mutane da kuma harkallar da makamai.

A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, Chiemeka Arinze ya mutu ne a ranar Juma’a, 26 ga watan Nuwamba, 2021.

Majiyar ta ce lauyan wanda ake karan ya shigar da kara ne a gaban kotu a makon da ya gabata, kan rashin lafiyar wanda yake karewa.

Majiyar ta kuma ce a yau litinin ne za a ci gaba da shari’a a kan batun, kuma an shirya a saurari bukatar belin wanda ake tuhuma kafin a ji labarin mutuwarsa.

An tattaro cewa Arinze, wanda aka ce bai da lafiya, an garzaya da shi daga gidan yarin zuwa wani babban asibiti a ranar Juma’a, inda daga bisani ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda SaharaRepoters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

Jerin wasu shari'o'i 17 na kisan gilla da ba a warware su ba a Najeriya har yanzu

A rahoton mu na baya, kun ji cewa, tsawon shekaru, an kashe 'yan Najeriya da yawa yayin da hukumomin tsaro ba su gano wadanda suka kashe su ba.

A cikin wannan kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito, Legit.ng ta lissafa wasu daga cikin wadannan shari'o'in kisan kai da kisan gilla wadanda har yanzu ba a bayyana makasan ba.

Daga cikin shari'o'in da ke hannun kotu har zuwa yanzu, Legit.ng Hausa a baya ta tattaro muku har da ta su Evans da tawagarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel