Da Duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa motar kwamishina wuta a Kogi

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa motar kwamishina wuta a Kogi

  • Wasu masu garkuwa da mutane sun farmaki motar kwamishinan jihar Kogi, sun harbe shi a kafarsa
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, kwamishinan yana kan hanyarsa ta zuwa Lokoja ne lokacin da aka farmake shi
  • An kuma sace wasu masu ababen hawa da suke kan hanyar, amma an ce kwamishinan ya tsallake ba a sace shi ba

Kogi - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun harbe kwamishinan muhalli na jihar Kogi, Adewale Omofaiye a kafa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Lahadi a tsakanin yankin Ikoyi da Iyara na jihar yayin da Omofaiye ya tsallake rijiya da baya, amma tare da harbin bindiga a jikinsa.

An ce mutane uku ne a cikin motar lokacin da suke kan hanya, wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka farmake su.

Kara karanta wannan

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

Taswirar jihar Kogi
Da Duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa motar kwamishina wuta a Kogi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai an ce kwamishinan yana cikin yanayi mai kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

SaharaReporters ta gano cewa wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun budewa motarsa wuta a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Lokoja, inda harsashi ya same shi a kafarsa.

Rahoto yace, an yi garkuwa da wasu masu ababen hawa inda aka tafi dasu cikin daji.

The Guardian ta ce, lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, (PPRO), DSP William Ayah, ya ce rundunar ba ta samu labari game da harin ba.

A halin da ake ciki wata majiya ta kara tabbatar da cewa shugaban karamar hukumar Ijumu kuma shugaban ALGON na jihar, Hon. Isah Taufiq, ya tattara ’yan banga da mafarauta domin kamo masu garkuwa da mutane da ceto wadanda aka sace.

Kara karanta wannan

Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

A wani labarin, an harbe wasu mutane biyu mazauna kauyen Durbi da ke gundumar Shere a karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato yayin da suke fafatawa da masu garkuwa da mutane.

Maharan, a cewar mazauna garin, sun bude wuta kan mutanen da ke bibiyarsu daga maboyarsu. Wasu da dama kuma an ce sun samu raunuka a lamarin.

Wadanda suka mutun dai sun hada da Peter Inyam da Arin Kaze.

Asali: Legit.ng

Online view pixel