Jirgin yakin sojojin NAF ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

Jirgin yakin sojojin NAF ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

  • Jirgin yakin rundunar sojin sama NAF na Operation Haɗin Kai sun aika dandazon mayakan ISWAP Lahira a Borno
  • Rahotanni sun bayyana cewa sojin sun gano tawagar masu karban haraji hannun mutane, inda suka sakar musu ruwan bama-bamai
  • Kazalika a wani cigaban kuma, sojojin kasa da yan sa kai sun hallaka mayakan ISWAP da dama a Marte

Borno - Jirgin yakin rundunar soji ta Operation Haɗin Kai, ya hallaka masu karban haraji na kungiyar ISWAP a karamar hukumar Kukawa, jihar Borno.

Daily Nigerian tace masu karban harajin, waɗan da ke tafiya cikin tawaga, sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke kan hanyar shiga ƙauyuka karban haraji a hannun mutane da yan kasuwa.

Jirgin yaki
Jirgin yakin sojojin NAF ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wani jami'in tsaro da ya nemi a boye bayanansa, ya shaida wa PRNigeria cewa:

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya tsayar da lokacin da za a yi taron gangamin APC na kasa

"An aiwatar da harin luguden wutan ta sama ne a kauyukan Tambuwan Marta da Mangari dake kusa da Baga a karamar hukumar Kukawa, jihar Borno."
"Zuwa yanzun bamu san adadin yawan yan ta'addan da suka sheka lahira ba, amma sun zarce 12."

Sojojin ƙasa sun kashe mayakan ISWAP

Kazalika a wani musayar wuta na daban, Sojoji sun samu nasarar hallaka mayakan kungiyar ISWAP da yawan gaske a yankin Marte.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin gwabzawa da yan ta'addan, sojoji hudu da sojan sa kai na JTF ɗaya sun samu raunuka daban daban.

Sai dai tuni aka garzawa da jami'an tssaron da suka jikkata zuwa Asibiti domin kulawa da lafiyarsu.

A wani labarin na daban kuma Gwarazan yan sanda sun ceto matafiyan da yan bindiga suka sace a hanyar Kaduna-Abuja, Mutum daya ya mutu

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da dimbin matafiya a hanyar Kaduna/Abuja

kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, Abdullahi Mudassiru, ya bayyana cewa yan sanda sun ceto matafiya 11 da aka sace a hanyar Kaduna-Abuja.

Kwamishinan yace yan sanda sun gano motar mutum ɗaya da ya mutu a harin, Alhaji Muhammadu Hamidu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel