'Yan APC mashaya barasa ne, su suke sukar ayyuka na a Benue, gwamna Ortom

'Yan APC mashaya barasa ne, su suke sukar ayyuka na a Benue, gwamna Ortom

  • Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya caccaki 'yan jam'iyyar APC a jiharsa, inda ya kira su da mashaya barasa
  • Gwamnan ya bayyana haka ne jiya Asabar, lamarin ya kuma kawo cece-kuce daga 'yan jihar tasa ta Benue
  • Gwamnan ya bayyana dalla-dalla cewa, 'yan APC ne ke kitsa komai na batanci da jawo masa zagi a jihar

Benue - Biyo bayan cece-kucen da ya biyo bayan kalaman da ya yi kan wasu ‘yan jiharsa da ya bayyana a matsayin 'yan barasa, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi karin haske.

A lokacin da yake kaddamar da sabon ginin Cocin Embassy na RCN a Makurdi, babban birnin jihar Benue, gwamnan ya ce wasu ‘yan jiharsa da ke wuni suna shan barasa suna ci gaba da cin mutuncinsa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom
'Yan APC ne mashaya barasa da ke sukar ci gaban da nake kawowa jihata, gwamna Ortom | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da dama dai sun bayyana hakan a matsayin abin da bai kamata ba, inda suka soki gwamnan da kuma zarginsa da rashin mutunta ‘yan jihar.

Sai dai a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Nathaniel Ikyur ya fitar a madadin sa, gwamnan ya ce batun na tsokaci ne ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a Benue.

Ikyur ya ce kalaman Ortom kan wasu mutane ne da suka kulla sharri a cikin zukatansu akansa.

"Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa labarin, musamman mai taken labarin ba gaskiya bane gaba daya da kuma kokarin bata sunan gwamnan."
“Gwamnan ya bayyana karara cewa mafi yawan al’ummar Benue sun sani kuma sun yaba da gagarumin ci gaban da yake kawo musu."

Gwamnan Benue: Ubangiji ne ya zo min yace na sake tsayawa takarar gwamna

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue: Ubangiji ne ya zo min yace na sake tsayawa takarar gwamna

Kafin karin bayanin, Samuel Ortom ya ce tun farko bai so sake tsayawa takara a zaben 2019 saboda zagin da yake sha daga 'yan adawar sa.

Ya kuma bayyana cewa, shi zababben ubangiji ne, don haka 'yan jihar tasa ya kamata su daina zaginsa haka siddan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce sai da yayi azumin wata uku, inda ya ce ubangiji ya ba shi umarnin sake tsayawa takarar gwamna.

Akume ya roki EFCC ta yi ram da gwamnan Benue Ortom ta bincikeshi kan wasu kudi

A baya kadan, ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sanata George Akume, ya nemi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su binciki Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Akume, tsohon gwamnan jihar Benue, ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin 30 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

Ya kuma nemi Ortom da ya daina fadan bakaken maganganu kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel