Akume ya roki EFCC ta yi ram da gwamnan Benue Ortom ta bincikeshi kan wasu kudi
- Tsohon gwamnan jihar Benue, Geoge Akume ya bukaci EFCC su bincike gwamna Ortom na jihar ta Benue
- Ya bayyana haka yayin da yake tataunawa da manema labarai a ranar Litinin 30 ga watan Agusta
- Akume ya kuma yi kira ga gwamna Ortom da ya gaggauta neman afuwar shugaba Buhari bisa kalaman batanci
Benue - Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sanata George Akume, ya nemi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su binciki Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.
Akume, tsohon gwamnan jihar Benue, ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin 30 ga watan Agusta.
Ya kuma nemi Ortom da ya daina fadan bakaken maganganu kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ortom yana fada da fadar shugaban kasa kan rikicin manoma da makiyaya da rashin tsaro a jiharsa ta Benue.
A bayanin Akume, ya bayyana cewa:
"Muna kira ga Gwamna Samuel Ortom da ya nemi afuwar Shugaba Muhammadu Buhari ba tare da bata lokaci ba, saboda amfani da kalamai marasa dadi da kuma yin aiki a waje da ka'idojin aiki tsakanin jihar da Gwamnatin Tarayya.
“Muna kira ga EFCC da ICPC da su binciki aikace-aikacen jumillar kudaden da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar Benue daga ranar 29 ga Mayu, 2015 zuwa yau.
“Ya kamata Gwamnatin Tarayya cikin gaggawa ta bada umarnin rusa rundunonin hana kiwon dabbobi a jihar Benue saboda shigarsu cikin ayyukan zalunci da ta'addanci da ke haifar da rushewar zaman lafiya da kisan gilla ga mutanen jihar Benue."
Taron ya samu halartar dattawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Benue.
NBC Ta Tuhumi Channels TV Kan Tattaunawa da Gwamna Ortom
Hukumar kula da kafafen watsa labarai ta ƙasa (NBC), ta tuhumi Channels tv kan maganganun da Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya yi a shirinta na Sunrise daily ranar Talata.
Hukumar NBC ta bayyana hakane a wata takarda da ta aike wa kafar watsa labaran, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Takardar tana ɗauke da kwanan watan 24 ga watan Agusta, kuma shugaban hukumar NBC, Balarabe Ilelah, ya saka hannu.
Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan kasuwa da Fulani makiyaya a jihar Delta
A baya, kun ji cewa, rikici ya barke a yankin Sapele, Karamar Hukumar Sapele ta jihar Delta yayin da ‘yan kasuwa Hausawa da Fulani makiyaya a yankin a ranar Litinin suka yi artabu da kare-jini-biri-jini a Kasuwar Hausa da ke kan hanyar Benin zuwa Warri, Amukpe, a cikin birni.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce akalla mutane goma ne suka samu munanan raunuka a cikin farmakin da ya biyo baya sannan aka garzaya da su asibitoci daban-daban a yankin, in ji rahoton Daily Report Nigeria.
Punch ta ruwaito cewa, an lalata shagunan katako, lamarin da ya haifar cunkoson ababen hawa yayin da wasu masu ababen hawa suke tsere suka bar ababen hawansu domin tsira.
Asali: Legit.ng