Innalillahi: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

Innalillahi: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

  • Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa an tsinci gawar wasu mutum biyu, mace da namiji a cikin mota
  • Hukumar yan sanda tace namijin yana da mata har da ƴaƴa, yayin da ita kuma macen za'a ɗaura mata aure a watan Disamba
  • A halin yanzun jami'an yan sanda na cigaba da bincike kan lamarin bayan likita ya tabbatar da mutuwar mutanen

Kano - An tsinci gawarwakin wasu mutum biyu, mace da namiji, a cikin wata mota a kan hanyar Katsina dake karamar hukumar Fagge, jihar Kano.

Wani shaidan gani da ido, ya shaida wa jaridar Dailytrust cewa an gano bayanan mutanen, Steven Ayika, wanda yana da aure har da ƴaƴa biyu, da kuma Chiamaka Emmanuel, wacce za'a yi bikinta a watan Disamba.

Shaidan ya bayyana cewa gilashin motar baki ne kuma an aje ta a gaban gidan Chiamaka dake kusa da hanyar Katsina.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 5 da za'a ka iya kare ban dakin zamani daga macizai

Jihar Kano
Innalillahi: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa sun garkame motar ta ciki kuma wayoyinsu duk a kashe yayin da aka gane abinda ke faruwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan sanda sun tabbatar

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, yace tawagar yan sanda ta dira wurin bayan samun rahoto.

Kiyawa ya bayyana cewa ba tare da ɓata lokaci ba jami'ai suka kai mutanen biyu Asibiti, inda likita ya tabbatar da cewa sun mutu.

PM News ta rahoto Kakakin yan sandan yace:

"Ranar 23 ga watan Nuwamba da misalin 4:50 na yamma, mun samu rahoton cewa an ga wata mota a gefen hanyar Katsina yankin karamar hukumar Fagge, jihar Kano. Akwai mace da namiji a motar kuma ba su motsi."
"Bayan samun rahoton, kwamishinan yan sanda, reshen jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya tada tawaga ta musamman zuwa wurin."

Kara karanta wannan

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

"Yan sandan sun gaggauta zuwa wurin, suka zaro mutum biyu mace da namiji a cikin motar Sienna, sannan suka kai su asibitin koyarwa na Murtala Muhammad, likita ya tabbatar da sun mutu."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kiyawa ya kara da cewa binciken da suka yi, ya nuna cewa mamacin namiji, Steven Ayika, yana zaune ne a Jaba Quarters jihar Kano. Sai kuma Chiamaka Emmanuel, ita ma Anguwarsu ɗaya.

Bugu da kari kakakin yan sandan ya tabbatar da cewa a halin yanzun jami'ai na cigaba da bincike kan lamarin.

A wani labarin na daban kuma yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda su gaggauwa kawo miliyan N200m kafin su bar wurin sabis

Yan bindigan da suka sace matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun nemi iyalan wani ɗan sanda su biya fansa.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun nemi a tattara musu miliyan N200 cikin awanni 6 kafin su bar gurin sabis.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Asali: Legit.ng

Online view pixel