Hanyoyi 5 da za'a kare ban dakin zamani daga macizai

Hanyoyi 5 da za'a kare ban dakin zamani daga macizai

Ranar Juma'ar da a gabata, wata jami'ar hukumar mayakan saman Najeriya, Lance Kofur Bercy Ogah, ta gamu da ajalinta cikin ban daki yayinda macijiya ta cijeta a gidanta.

Jami'ar ta fuskanci cizon macijiyar ne yayinda take biyan bukatarta a bayin gida cikin barikin Sojin NAF Base dake Abuja.

Punch ta ruwaito cewa bayan cizon, Kofur Ogah ta kwashe yaran dake gidanta kuma ta kaisu wajen makwabta sannan ta garzaya asibitin Nigerian Air Force hospital amma lokaci ya yi.

A shekarar nan kadai, mutane da dama sun yi arangama da macizai cikin ban dakinsu.

Macizai na shiga ban daki ta sokaway, pipe, da salanga.

Amma ba macizai kadai ke shiga wadanda wurare ba, akwai kadangari, tsutsosi da beraye.

Kara karanta wannan

Bidiyon Macijiyar da ta hallaka jami'ar Soja cikin ban daki a Abuja

Hanyoyi 5 da za'a ka kare ban dakin zamani daga macizai
Hanyoyi 5 da za'a ka kare ban dakin zamani daga macizai
Asali: UGC

Legit ta tattaro muku hanyoyi 5 da zaka iya kare ban dakinka daga macizai:

1. Yi amfani da ragar karfe wajen rufe dukkan wani wajen da ruwa ke iya shiga cikin ban daki

2. Sanya magani cikin magudanar ruwan ban daki akalla sau biyu a shekara

3. Kada ka bar sokaway na gidanka a bude

4. Gyara dukkan wani pipe da ya balle. Barinsu a lalace na da hadari

5. Leka cikin bayi kafin ka zauna kuma ka tabbatar akwai haske

Asali: Legit.ng

Online view pixel