Rahoto: 'Yan Zamfara sun shiga damuwa, 'yan bindiga sun fara karbar harajin noma

Rahoto: 'Yan Zamfara sun shiga damuwa, 'yan bindiga sun fara karbar harajin noma

  • Mazauna karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara suna kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki dangane da tsaron rayuwarsu
  • Mazauna yankin sun yi ta kokawa a baya-bayan nan dangane da matakin da ‘yan bindiga suka dauka a yankunansu, inda suka yi kira ga gwamnati ta kawo dauki
  • A halin da ake ciki, mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindiga na lalata gonakinsu tare da saka musu harajin dole

Zamfara - Harin da ‘yan bindiga suke kai wa a jihar Zamfara ya fara daukar wani sabon salo inda suka fara karbar kudi a wasu kauyuka.

Rahotanni na baya-bayan nan na nuni da cewa a halin yanzu ‘yan bindigar na karbar haraji daga hannun jama’a ta hanyar kafa shingayen kan titi.

Gwamnan jihar Zamfara, Matawalle
Jama'a sun yi ta kururuwa yayin da 'yan bindiga suka yi sabon yunkuri, suna karbar haraji a Zamfara | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mazauna garin Magami dake karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara sun koka kan tabarbarewar tsaro, inda suka roki gwamnati da ta taimaka ta ceto su daga barnar ‘yan bindiga da suka sanya musu haraji.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Sabuwar kungiyar tsageru ta kai hari kamfanin man fetur a jihar Ribas

A cewarsu, ‘yan bindigan kan dasa shingen ne domin karbar kudaden haraji, inda suke kukan cewa duk wanda ya kasa biyan harajin, za a lalata gonarsa kuma a sace shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Suka ce:

"Idan ka kasa biyan 'yan bindiga kudaden haraji, ko dai su sace ka ko kuma su kona gonar ka."

Sai dai, jaridar ta ci gaba da cewa, rundunar ‘yan sandan jihar ta musanta rahoton, inda ta ce ba a kai wasu korafe korafe gabanta ba na lalata gonakin da ‘yan bindigan suka yi.

Matakin baya-bayan nan da 'yan bindiga suka dauka

Wani dan asalin garin Magami ta bayyana a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa yankin na cikin wani mummunan bala’i.

A cewarsa:

“Da zarar ka tashi daga Gusau kafin ka isa Magami aiki ne mai wuyar sha’ani, sai dai idan kana da ‘yan rakiya, tun lokacin da aka kashe aikin ‘yan sandan MOPOL a rana, suna tare hanya sau hudu zuwa biyar, suna tsayar da manyan motoci suna kwashe kayan da ke ciki. Suna kuma sanya haraji.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun saka wa mutane haraji, sun ce wanda bai biya ba zai yaba wa aya zaƙin ta

“Idan ka je Magami, kilomita daya zuwa Magami ‘yan bindiga za su iya tare ka, ko dai su sace ka ko kuma su ce ka biya haraji. Ya zuwa ranar Litinin sun kona gonaki biyu a garin Magami saboda rashin biyan haraji ga 'yan bindigan.

Koken manoma

“Manoman sun je girbin masara amma ‘yan bindiga sun tare su suka banka wa gonakin wuta. Sun yi garkuwa da wasu mata biyu. ‘Yan bindigan sun kwace wata sabuwar motar manoman, amma daga baya suka sako matan.
"‘Yan bindigan sun bukaci a basu kudi, kafin manoman su yunkura su biya, 'yan bindigan sun kona gonakin tare da yi musu barazanar cewa idan ba a ba su kudi ba za su ci gaba da kona gonakin."

Ya koka da cewa duk da cewa akwai sojoji da aka girke a garin Magami, amma mazauna garin sun dogara ga Allah Madaukakin Sarki domin shi kadai ne zai iya kare su.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake kai hari Filato, sun kashe mutane biyu

Ya kara da cewa:

"Wannan ita ce matsalarmu a kowace rana da damuwarmu ta yau da kullum."

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

A wani labarin, ana fargabar 'yan bindiga sun kashe mutane da yawa tare da kona dukiyoyinsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan wasu al'ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Harin wanda rahotanni suka ce ya fara ne da yammacin ranar Talata zuwa sanyin safiyar Laraba, yayi sanadiyyar kona gidaje da yawa da suka hada da gine-ginen gwamnati da motoci, Daily Trust ta ruwaito.

Shaidu sun ce akalla al’ummomi biyar ne ‘yan bindigar suka afkawa, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel