Kisan Musulmai a Jos: Majalisar malamai ta ce kada Musulmai su dauki doka a hannu
- Daga jihar Filato, rahoto ya bayyana cewa, majalisar Malamai ta hana musulmai kai farmaki kan kowa a jihar
- Majalisar ta bayyana haka ne yayin da take martani kan kisan da aka yiwa wasu matafiya a ranar Asabar
- Majalisar ta bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar sun kamo tare da gurfanar da wadanda suka aikata danyen aikin
Jos, Filato - Majalisar Malamai/Dattawa ta Jihar Filato ta yi kira ga al’ummar Musulmi da ke Jos da kada su kai farmaki kan kowa don daukar fansa kan kisan da aka yi wa musulmai a kan hanyar Gada-biyu - Rukuba, cikin Karamar Hukumar Jos ta Jihar Filato.
An kashe wasu Fulani matafiya musulmai a ranar Asabar a kan hanyarsu ta komawa jihohin Ondo da Ekiti bayan sun halarci wani hidiman addini a Bauchi, an kai musu hari inda aka kashe sama da 20, mutane da yawa sun ji rauni kuma kusan 10 sun bace.
A rahoton Daily Trust, ta ce wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar, Ahmad Muhammad Ashir ya ce:
"Musulunci bai goyon bayan tashin hankali saboda haka bai kamata a kai hari ko kashe wani da sunan daukar fansa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Duk da cewa abin takaici ne kuma da radadi a tare matafiyan Fulani marasa laifi, a fitar da su daga cikin motocin bas din su, sannan mahara su yi amfani da makamai su hallaka su, hakan bai kamata ya ba mutane damar yin haka akan masu wucewa ko matafiya ba.
“Mu a majalisa mun yi tir da harin da kashe-kashen baki daya kuma muna kira da a kama su duka sannan a binciki wadanda suka aikata wannan danyen aikin don gurfanar da su.
“Majalisar Malamai/Dattawa na kira ga dukkan Musulman Filato da su kwantar da hankulan su kada su dauki doka a hannun su.
“Muna yabawa dukkan hukumomin tsaro kan irin kokarin da suka yi cikin gaggawa; Muna kuma godiya da kokarin Gwamna Simon Lalong, Gwamna Rotimi Akeredolu, da Shugaba Muhammadu Buhari wajen tabbatar da cewa lamarin bai yi muni ba."
Ba ma son a kama sunan wani kan kisan musulmai a Jos, Kwamishinan 'yan sandan Filato
Kwamishinan ‘yan sandan Filato, Edward Egbuka, ya ce duk da cewa harin da aka kai kan matafiya a Jos ranar Asabar ba shi ne karon farko da irin wannan lamarin ya faru ba, 'yan sanda ba sa son a kama sunan kowa a lamarin.
Ya lura cewa wadanda suka kai farmaki kan matafiyan a Jos a ranar 14 ga watan Agusta 'yan ta'adda ne da 'yan daba wadanda ke son dagula yanayin tsaro a jihar don haifar da matsala da sace-sace.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Shugaban hukumomin tsaro a jihar ga Gwamna Simon Lalong.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Gwamna Dr Makut Macham ya fitar a Jos, Punch ta ruwaito.
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos
A wani labarin, Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.
Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.
Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.
Asali: Legit.ng