'Yan bindiga sun dira gonar wasu mutane yayin da suke girbi, sun tafka aika-aika

'Yan bindiga sun dira gonar wasu mutane yayin da suke girbi, sun tafka aika-aika

  • Wasu masu garkuwa da mutane sun farmaki gonar wasu 'yan uwa, inda suka sace su tare da hallaka mutum daya
  • A halin da ake ciki, an ajiye gawar mamacin a asibiti yayin da ake kokarin nemo wadanda aka sacen
  • Rahoto daga majiyoyi sun bayyana yadda lamarin ya faru har masu garkuwa da mutanen suka hallaka mutumin

Kogi - Masu garkuwa da mutane sun kashe wani mutum mai suna Ayuba, tare da yin garkuwa da wasu ‘yan uwansa shida a cikin wata gonarsu da ke unguwar Lagbeta a karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, al’ummar Labgeta na kan hanyar Abuja zuwa Lokoja da ake yawan hada-hada.

Taswirar jihar Kogi
'Yan bindiga sun farmaki wasu dangi a gona yayin da suke girbi, an kashe mutum daya | Hoto: channelsv.com
Asali: Twitter

Dan uwan ​​wadanda abin ya shafa Ishaya Bulus, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Laraba da misalin karfe 10:12 na safe a lokacin da dangin ke girbin amfanin gona.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

Ya ce masu garkuwa da mutane sun harbe daya daga cikin ‘yan uwan a lokacin da yake kokarin tserewa a lokacin da ake shiga dasu daji.

A cewarsa:

"Suna cikin girbin amfanin gona, sai ga masu garkuwa da mutane sun fito kwatsam suka zagaye su da bindiga."
“A lokacin da suke shiga da wadanda abin ya shafa cikin daji ne daya daga cikinsu ya yi yunkurin tserewa, nan ne daya daga cikin masu garkuwar ya bude masa wuta."

Ya ce an ajiye gawar wanda ya mutu a dakin ajiyar gawa, kuma a cewarsa har yanzu ‘yan uwan ba su samu wata alaka ta tattaunawa da masu garkuwa da mutanen ba.

Wata 'yar banga a karamar hukumar Kotonkafe, wacce ta so a sakaya sunanta, ta tabbatar da faruwar lamarin, duk da cewa ta ce ‘yan banga na zagaya dajin domin gano maboyar barayi.

Kara karanta wannan

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran wayarsa ba, sannan kuma bai dawo da sakon tes da aka tura masa ba.

'Yan bindiga da masu garkuwa da mutane na ci gaba da barna a yankuna daban-daban na kasar nan.

A makon nan ne wasu manoma suka bayyana irin wahalhalun da suke fuskanta daga 'yan bindiga a sassan jihar Zamfara.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, 'yan bindigan sun fara saka wa mazauna Zamfara haraji yayin da suke aikin kwashe kayan gona.

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

A wani labarin, ana fargabar 'yan bindiga sun kashe mutane da yawa tare da kona dukiyoyinsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai kan wasu al'ummomi a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Harin wanda rahotanni suka ce ya fara ne da yammacin ranar Talata zuwa sanyin safiyar Laraba, yayi sanadiyyar kona gidaje da yawa da suka hada da gine-ginen gwamnati da motoci, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Shaidu sun ce akalla al’ummomi biyar ne ‘yan bindigar suka afkawa, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel